Sanusi II Ya Magantu kan Rigimar Matatar Dangote da NNPCL, Ya Gano Masu Laifi
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi Allah wadai da yadda ake neman kawo cikas ga matatar Aliko Dangote a Najeriya
- Sanusi ya nuna damuwa kan yadda ake kokarin kawo cikas ga matatar da za ta jawo abubuwan cigaba ga Najeriya baki daya
- Basaraken ya zargi wasu manya da hannu a rigimar domin cigaba da cin ribarta musamman game da farashin mai a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan abin da ke faruwa da matatar Aliko Dangote.
Sanusi II ya ce abin takaici ne yadda aka sako matatar a gaba inda ya ce ana yin haka ne domin dakile cigaban da za ta kawo.
Sanusi II ya magantu kan matatar Dangote
Basaraken ya fadi haka ne yayin kaddamar da littafi a Abuja da tsohon Minista, Shamsudden Usman ya wallafa ta hadin guiwa, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, sarkin ya koka kan halin yan Najeriya duba da yadda suke neman kwashe dukiyar kasar ba tare da neman hanyar inganta ta ba.
Sanusi II ya zargi wasu manya a kasa jawo wannan rigima domin biyan bukatun kansu, The Guardian ta ruwaito.
Sanusi II ya koka kan halin yan Najeriya
"Kasar Najeriya ta gamu da wasu mutane da ke amfani da ita wurin cin riba madadin kawo mata cigaba."
"Wannan shi ne gaskiyar abin da ya kashe Najeriya, mutane suna shiga ofis abin da suke fara tunani shi ne nawa za su samu daga gare ta."
"Ba wai damuwarsu ta yaya za su bautawa kasar da kuma da alummarta ba wanda abin takaici ne matuka."
- Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya bukaci addu'a ga Dangote, BUA
A wani labarin, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya roki ubangiji ya hada kan attajiran jihar guda biyu domin kawo mata cigaba.
Sanusi II ya kuma roki al'umma su dage da addu'o'i domin Allah ya hada kan attajiran Kano, Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu.
Basaraken ya ce duk mai neman kawo rigima tsakanin attajiran na Kano ba son cigaban jihar ya ke yi ba ko kadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng