“Akwai Matsala”: Sarakuna Sun Roki Tinubu Alfarma game da Yahaya Bello

“Akwai Matsala”: Sarakuna Sun Roki Tinubu Alfarma game da Yahaya Bello

  • Gamayyar sarakunan gargajiya a jihar Kogi sun nuna damuwa kan yadda rayuwar tsohon gamna, Yahaya Bello ke cikin hatsari
  • Sarakunan sun bayyana cewa ana kokarin ganin bayan Yahaya Bello inda suka roki shugaba Bola Tinubu alfarma
  • Wannan na zuwa ne yayin da hukumar EFCC ke cigaba da tuhumar tsohon gwamnan kan zargin badakalar makudan kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wasu sarakunar gargajiya a jihar Kogi sun bayyana yadda ake kokarin hallaka tsohon gwamna, Yahaya Bello.

Sarakunan suka ce yadda hukumar EFCC ke tafiyar da lamarin Yahaya Bello abin kunya ne ga Najeriya.

Sarakuna sun roki Tinubu kan halin da Yahaya Bello ke ciki
Wasu sarakuna a jihar Kogi sun nuna damuwa kan halin da Yahaya Bell ke ciki. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Alhaji Yahaya Bello.
Asali: Facebook

Sarakuna sun roki Tinubu kan Yahaya Bello

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar 26 ga watan Satumbar 2027, cewar The Cable.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke da dattawa suka kalubalanci gwamna kan nadin sabon sarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarakunan sun bukaci shugaba Bola Tinubu da ya shiga lamarin wurin tabbatar da EFCC sun bi doka.

Masu rike da sarautun gargajiyan sun bayyana cewa abin takaici ne yadda EFCC ke tafiyar da shari'ar Yahaya Bello, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sarakunan sun koka kan cin zarafin Yahaya Bello

'Mai girma shugaban kasa, danmu yana cikin hatsari, mu na da tabbacin kai mai son dimukradiyya ne da ke son inganta Najeriya."
"Abubuwan cigaba da ka kawo a kankanin lokaci a bayyanae suke, hakan ba zai bata dukan abubuwan da aka yi ba, duba da yadda EFCC ke cin zarafin danmu."

- Cewar sanarwar

Mai girma Attah na Igala shi ya sanyawa wasikar hannu da sauran manyan sarakunan gargajiya a jihar.

Sauran su ne Sanatan Kogi ta Gabas, Jibrin Echocho da kakakin Majalisar jihar, Aliu Yusuf da sauran yan siyasa.

Kara karanta wannan

Zargin N27bn: Bayanai sun fito da hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamna

EFCC: Kotu ta dage shari'ar Yahaya Bello

Kun ji cewa Babbar kotun tarayya, mai zamanta a Abuja, ta dage sauraron zargin almundahana da ake yi wa tsohon gwamna, Yahaya Bello.

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ce ke zargin tsohon gwamnan da handame sama da N80bn daga asusun Kogi.

Mai Shari'a Emeka Nwite ya dage sauraron shari'ar zuwa watan Oktoba, inda ake jiran hukuncin kotun koli kan karar da Bello ya shigar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.