Dalilan da Suka Jawo Fetur Yake Tsada duk da Samuwar Matatar Dangote Inji Injiniya

Dalilan da Suka Jawo Fetur Yake Tsada duk da Samuwar Matatar Dangote Inji Injiniya

  • A watan nan aka fara tace danyen mai a matatar Dangote da ke garin Legas bayan shekaru ana dogon jira
  • Mutane sun ci burin fetur zai sauko tun da an huta daga sayo shi daga ketare, amma sai aka ji akasin haka
  • Wani wanda ya fahimci kasuwar mai da tattalin arziki ya jero dalilan da suka jawo ake sayen fetur da tsada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A lokacin da ake shigo da mai daga waje, mutane da yawa sun fahimci hikimar da ta jawo fetur ta ke yin tsada a Najeriya.

Ganin an fara tace mai a matatar Dangote amma festur bai sauko ba, jama’a sun fara mamakin yadda kasuwar ta ke aiki a kasar nan.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya shiga matsala, an yi wa layin wayarsa kutse a Najeriya

Dangote
Dangote ya fara tace mai amma har yau fetur na tsada a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abubuwan da suka hana feturin Dangote araha

M. S Ingawa wanda ya fahimci harkar tattalin arziki musamman abin da ya shafi man fetur ya yi bayani a shafinsa na X a can kwanaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A maimakon a ji litar fetur ta sauka kasa tun da an huta da jigila da dako daga ketare, sai aka ji kamfanin NNPCL ya sanar da karin kudi.

Injiniya M. S Ingawa ya yi bayani mai gamsarwa a dandalin da aka fi sani da Twitter, ya ce ya kamata a fahimci kasuwancin danyen mai.

Duk da ana hakar man ne a nan, ya ce ana yi wa danyen mai farashi ne da lissafin kasuwar duniya da siyasar duniya ta saba juya shi.

Masanin ya kuma nuna za a kashe kudin tace danyen man a matata kuma kamfanin Dangote ya nemi riba tun da kasuwanci ya fito yi.

Kara karanta wannan

'Zai kara aure?': Al'umma sun bayyana ra'ayoyi kan sakin Seaman Abbas

Tashar AIT ta fara yin hira da matashin domin jin abin abin da ya hana farahin fetur sauka.

Dangote: Tashin Dala zai hana fetur araha

Wani abin dubawa wajen tsaida farashin shi ne farashin Dala da sauran kudin waje. A yanzu darajar Naira ta karye a kasuwar canji.

Abin bai tsaya nan ba, dole 'yan kasuwan da suke sayen man daga matata a kan sari su daura riba da kudin jigila zuwa gidajen mai.

Sannan ya ce hukuma ta kan karbi kudi idan an yi cinikin mai ko gas a tara a asusun MDGIF, ana karbar kudin ne ta hannun NDMDRPA.

Dangote ya yi kuskure kan farashin fetur

Ana da labari cewa Alhaji Aliko Dangote ya ce feturin Saudiya ya fi na Najeriya tsada, wanda hakan ya sa aka duba gaskiyar zancen.

Binciken da aka gudanar ya nuna ikirarin dan kasuwar ba gaskiya ba ne domin kuwa farashin mai a Najeriya ya fi araha kan Saudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng