Zargin N27bn: Bayanai Sun Fito da Hukumar EFCC Ta Cafke Tsohon Gwamna

Zargin N27bn: Bayanai Sun Fito da Hukumar EFCC Ta Cafke Tsohon Gwamna

  • Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a yau Juma'a
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama tsohon gwamnan ne a gidansa da ke kan zargin laifuffuka 15
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da badakalar biliyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci a Najeriya (EFCC) ta cafke tsohon gwamnan jihar Taraba.

Hukumar EFCC ta yi nasarar cafke Darius Ishaku ne kan zargin badakalar makudan kudi har N27bn.

EFCC ta cafke tsohon gwamnan Taraba
Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku kan badakalar N27bn. Hoto: Architect Darius Ishaku.
Asali: Twitter

EFCC ta kama tsohon gwamna, Darius Ishaku

TVC News ta ruwaito cewa an cafke tsohon gwamnan ne a yau Juma'a 27 ga watan Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": Sarakuna sun roki Tinubu alfarma game da Yahaya Bello

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta ruwaito cewa hukumar EFCC za ta gurfanar da Darius Ishaku a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana tuhumar tsohon gwamnan da laifuffuka har guda 15, cewar Premium Times.

Darius Ishaku ya mulki jihar Taraba ne a karkashin jam'iyyar PDP daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Wata majiya daga hukumar EFCC ta ce:

"Tabbas yana hannunmu, muna cigaba da bincikensa tun lokacin da ya ke gwamnan jihar Taraba."
"Akwai wasu zarge-zarge a kan tsohon gwamnan na makudan kudi."

Arangamar EFCC da Yahaya Bello

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke zargin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da zargin badakalar biliyoyi.

Hukumar na zargin Yahaya Bello da karkatar da N82bn lokacin da ya ke mulkin jihar kafin karin wasu zarge-zarge.

A kwanakin nan hukumar ta sha arangama da tsohon gwamnan inda kai masa samame a gidansa da ke birnin Abuja.

Kara karanta wannan

"Sai ka gurfana a gaban kotu:" Hukumar EFCC ta kalubalanci Yahaya Bello

EFCC ta firgita mutane yayin kama Yahaya Bello

Kun ji cewa an shiga firgici bayan jin karar harbe-harbe da ake zaton na EFCC ne a kokarin cafke tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana zaton jami'an hukumar EFCC ne ke harbin a kokarin cafke tsohon gwamnan a Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan shafe tsawon lokaci hukumar na neman Yahaya Bello kan karkatar da makudan kudi har N80.2bn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.