"Da Wuya a Magance Rashin Tsaro:" Obasanjo Ya Gano Abin da ke Barazana ga Kasa

"Da Wuya a Magance Rashin Tsaro:" Obasanjo Ya Gano Abin da ke Barazana ga Kasa

  • Tsohon shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo ya dora alhakin ta'addanci kan rashin ilimi
  • Ya koka kan yadda aka samu yara sama da miliyan 20 da ba sa zuwa makarantar boko a kasar nan
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana wasu hanyoyi da za a bi wajen magance rashin tsaron Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Oyo - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce nan gaba kadan matsalar rashin tsaro za ta fi karfin gwamnati matukar ba a dauki mataki ba.

Tsohon shugaban ya nusar da kasar nan cewa yara marasa zuwa makaranta a yanzu su ne za su kara lalata tsaron kasar nan a gaba.

Kara karanta wannan

Bayan zarginta da jefa jama'a a wahala, gwamnati ta fadi alfanun cire tallafin fetur

Obasanjo
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana barazanar rashin tsaro Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Jaridar The Guardian ta tattaro cewa tsohon shugaba Obasanjo ya fadi haka ne yayin taron makarantar Apata Community Grammar School da ke Ibadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun Obasanjo ya fadi dalilin kamarin rashin tsaro

Cif Olusegun Obasanjo ya ce rashin tsaron da ake fama da shi a Najeriya ya samo asali daga yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihohi.

Tsohon shugaban Najeriya ya koka kan yadda alkaluma su ka nuna cewa yan kasar nan sama da 20,000,000 ne ba sa zuwa makaranta.

Obasanjo ya gano hanyar dakile rashin tsaro

Kawar da talauci ta hanyar samawa mutane ayyuka yi da sana'o'in hannu ga matasa ma daga hanyoyin da za a kawar da rashin tsaro a Najeriya, cewar Obasanjo.

Ya shawarci shugabannin kasar nan su yi abin da ya dace wajen tabbatar da yara sun samu guraben karatu, sannan matasa sun samu ayyukan yi.

Kara karanta wannan

Gangamin zanga zangar 1 Oktoba ya kankama, an mika bukatu ga Tinubu

An kama jami'i da taimakawa rashin tsaro

A baya kun ji yadda jami'an yan sandan jihar Zamfara su ka kama wasu mutane, ciki har da jami'in hukumar tsaron fararen hula bisa zargin taimakawa yan ta'adda.

Yan sandan sun kama jami'in NSCDC mai suna ACS II Maikano S/Tasha da alburusai da bindigar AK-47, da wani likitan bogi Mamuda Sani Makarari da alburusai da za a kai wa yan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.