Sanatan Najeriya, Orji Uzor Kalu Ya Rasu? Bayanai Sun Fito

Sanatan Najeriya, Orji Uzor Kalu Ya Rasu? Bayanai Sun Fito

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra, Sanata Orji Uzor Kalu ya dawo daga Amurka bayan shafe kwanaki da ya yi a kasar waje
  • Sanata Kalu ya yi magana kan raɗe radin da ake cewa ya mutu, inda ya ce ba jinya ce ta kai shi kasar waje balle ma ya mutu
  • Haka zalika Sanatan ya yi magana kan halin kuncin rayuwa da ake ciki a Najeriya inda ya ba shugaban kasa shawara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu ya dawo Najeriya bayan ya kwashe kwanaki yana karatu a kasar Amurka.

Sanata Orji Kalu ya yi bayanai kan abubuwan da suka faru a Najeriya musamman zaben gwamna da aka yi a jihar Edo.

Kara karanta wannan

'Zai kara aure?': Al'umma sun bayyana ra'ayoyi kan sakin Seaman Abbas

Sanata Kalu
Sanata ya musa cewa ya mutu. Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Sanata Kalu ya warware gaskiya kan zancen da aka yada cewa ya rigamu gidan gaskiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Kalu ya ce bai mutu ba

Sanata Orji Uzor Kalu ya ce masu cewa ya mutu a kasar Amurka ba su ma san menene ya kai shi kasar ba kwata-kwata.

Kalu ya bayyana cewa karatu ne ya kai shi kasar waje ba jinya ba balle ma ace ya mutu daga can a kasar Amurka.

Sanatan Abia ya yi magana kan zaben Edo

Vanguard ta wallafa cewa Sanata Kalu ya ce APC ta yi matuƙar kokari da ta kayar da jam'iyyar PDP mai mulki a zaben gwamna a jihar Edo.

Ya ce dole a yabawa shugaba APC, Abdullahi Umar Ganduje da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan nasarar.

Maganar Sanata Kalu kan tsadar rayuwa

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yiwa Jonathan martani kan tsige shi daga gwamnan CBN a 2013

A ɓangaren tattalin arziki, Sanata Kalu ya ce dole a yabawa Bola Tinubu kan kokarin da yake na farfaɗo da tattalin Najeriya.

Duk da haka ya bukaci shugaban kasar kan kawo sauki ga yan Najeriya domin a cewarsa ana cikin mummunan hali.

Kalu ya ce shi ba barawo ba ne

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa, shi ba barawo ba ne, kuma sam bai taba sata ba amma aka kakaba masa sata.

Sanata Orji Uzor Kalu ya ce kafin ya shiga siyasa ma yana da kudinsa, kuma ya yi tasiri wajen kafa jam’iyyar PDP mai adawa a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng