An Damke Jami'in Tsaron da ke Taimakon Yan Ta'adda a Zamfara

An Damke Jami'in Tsaron da ke Taimakon Yan Ta'adda a Zamfara

  • Jami'an yan sandan Zamfara sun cafke wani jami'in tsaron farar hula bisa zarginsa da taimakon yan ta'adda
  • An kama ACS II Maikano S/Tasha da alburusai da bindigar AK-47 zai kai wa wasu yan ta'adda a Zamfara
  • Haka kuma yan sanda sun kama matan rikakkun yan ta'adda guda biyu da alburusai za su kai kauyuka biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana nasarar damke wani jami'in hukumar tsaron fararen hula (NSCDC) bisa alaka da yan ta'adda.

An damke jami'in ne bisa zargin safarar makamai, alburusai da miyagun kwayoyi ga yan ta'addan da su ka addabi mazauna Zamfara da kewaye.

Kara karanta wannan

Dauda vs Matawalle: Gwamnati ta fara binciken masu daukar nauyin 'yan bindiga

Police
Yan sanda sun kama masu taimakon yan ta'adda Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Channels Television ta wallafa cewa an damke jami'in mai suna ACS II Maikano S/Tasha da alburusai da bindigar AK-47 da zargin zai kai wa yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zamfara: An cafke masu taimakon ta'addanci

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa an kama wani likitan bogi Mamuda Sani Makakari, wanda bincike ya nuna shi ke kula da lafiyar yan ta'addan.

Kwamishinan yan sandan Zamfara, Mohammed Dalijan ne ya tabbatar da haka, inda ya ce an samu alburusai 441 daga hannun Mamuda.

Yan sanda sun kama matan yan ta'adda

Kwamishinan yan sandan ya kuma bayyana cewa an kama wasu mata biyu, da aka tabbatar su na auren rikakkun yan ta'adda, Kachalla Jijji da Bello Kaura.

An kama su da rakiyar likitan bogi, Mamuda Sani Makarari dauke da da yara masu yawa a hanyarsu ta kai alburusai da makamai yankunan Anka da Bukkuyum a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami’an gidan yari 4, ta fadi dalili

Gwamnati na binciken masu daukar nauyin ta'addanci

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta fara binciken masu daukar nauyin ta'addanci da ya hana mazauna Zamfara da sauran sassan Arewa maso Yamma zaman lafiya.

Gwamnati ta fara binciken ne bayan yawaitar musayar yawu da zargin juna da daukar nauyin yan ta'adda a Zamfara, tsakanin Gwamna Dauda Lawal da karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.