Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70,000

Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70,000

  • Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000
  • Hakan na zuwa ne watanni bakwai bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin albashin ma'aikatan gwamnati
  • Kimanin ma'aikatan gwamnatin tarayya miliyan 1.2 ne za su fara samun albashin a watan Satumba da muke ciki daga yau Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja gwamnatin tarayya ta fara biyan mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000 a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan gwagwarmaya da kungiyoyin kwadago suka yi kan bukatar ƙarin albashi a Najeriya.

Albashi
Tinubu ya fara biyan sabon albashi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa albashin ma'aikatan gwamnatin tarayya zai dawo N4tn duk wata saboda karin kudin.

Kara karanta wannan

Ma'aikata sun cika da murna: Gwamna zai fara biyan sabon albashin N70000 a Oktoba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi karin albashin N70,000

Jaridar the Cable ta wallafa cewa ranaru Alhamis ma'aikatan gwamnatin tarayya za su fara samun sabon albashi na N70,000.

Daraktan yada labarai a ma'aikatar tattara kudi ta kasa, Bawa Mokwa ne ya tabbatar da haka ga manema labarai.

Ma'aikatan da za su samu karin albashi

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka hada da jami'an tsaro za su samu karin albashin.

Haka zalika malaman makarantun gaba da sakandare, ma'aikata a ofis ofis duk za su shiga cikin karin mafi ƙarancin albashin.

Ma'aikata sun fara samun sabon albashi

Wani ma'aikaci da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa a yanzu haka wasu ma'aikata sun fara samun sabon albashin.

A yanzu haka dai sauran ma'aikata za su cigaba da zuba ido domin ganin an biya su albashin watan Satumba da sabon mafi ƙarancin albashin.

Kara karanta wannan

Ranar 'yanci: Gwamnatin Tinubu ta lissafa muhimman ayyukan da ta yiwa talakawa

Tinubu zai fadada kofofin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta fitar da sanarwa kan wasu tsare tsare da ta kawo a kan tattalin arzikin Najeriya.

Hadimin shugaban kasa a kan tsare-tsaren haraji, Taiwo Oyedele ne ya fitar da sanarwar kan yadda sabon tsarin zai fara aiki a kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng