Seaman Abbas: Rundunar Soji Ta Sallami Sojan Ruwa da Aka 'Tsare' har Shekaru 6

Seaman Abbas: Rundunar Soji Ta Sallami Sojan Ruwa da Aka 'Tsare' har Shekaru 6

  • Bayan shekaru shida da ake zargin an tsare wani sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna, an samu rahoton yanzu sojan ya shaki iskar 'yanci
  • Rahoto ya nuna cewa Seaman Abbas ya fara samun sauki bayan kai shi asibiti, amma kuma rundunar soji ta kore shi daga aiki kan lamarin
  • Matar Abbas Haruna. Hussaina Iliya ta nuna matukar godiyarta ga dukkanin wadanda suka taimaka har mijinta ya kubuta daga ukubar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta saki Seaman Abbas Haruna wanda ake zargin an kulle shi na tsawon shekaru shida.

Sai dai kuma bayan shakar iskar sojan ruwan, rahoto ya nuna cewa rundunar ta sallame shi daga aikin soja inda a yanzu ya koma farar hula.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yiwa Jonathan martani kan tsige shi daga gwamnan CBN a 2013

Rahoto ya nuna cewa rundunar soji ta sallami Seaman Abbas daga aiki
Seaman Abbas ya shaki 'yanci amma rundunar soji ta kore shi daga aiki. Hoto: Brekete Family
Asali: Facebook

Seaman Abbas ya fara murmurewa

A wata hira ta kai tsaye da gidan talabijin na Brekete Family ya watsa wanda Legit Hausa ta bibiya, an fahimci cewa Seaman Abbas ya fara samun sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda akaji jagoran gidan talabijin din Ahmed Isa (Ordinary President) ya ke fada, an kai Seaman Abbas asibitin sojoji da ke Kaduna (44) domin jinyarsa.

Ahmed Isa ya ce bayan wata daya da kwanaki 10 aka sallami sojan ruwan kuma a yanzu ya murmure duk da cewa akwai sauran rashin lafiya a kwakwalwarsa.

Sojoji sun sallami Seaman Abbas

A cewar shugaban gidan rediyon, rundunar soji ta sallami Seaman Abbas daga aiki, inda aka sanya wata macen soja ta yi masa fareti zuwa kofar fita daga bariki.

Ahmed Isa ya ce har yanzu dai babu wata hukumar tsaro, ciki har da ita rundunar sojin ruwan kan tabbacin ko an kori Seaman Abbas daga aiki ko gudowa ya yi.

Kara karanta wannan

Fashin banki a Arewa: Kotu ta yankewa mutane 5 hukuncin kisa, bayanai sun fito

Sai dai ya ce sun samu bayanin cewa an dade da aka kori sojan ruwan daga aiki, kawai dai ba a rubuta takardar tabbatar da hakan ba ne a hukumance.

Matar Abbas ta yi wa jama'a godiya

Da ta ke jawabi bayan sako mijin nata, Hussaina Iliya ta godewa daukacin al'ummar Najeriya musamman Ahmed Isa bisa jajircewarsu har mijinta ya shaki 'yanci.

"Da ina ta kuka ni kadai, amma yanzu na samu masu tayani. Ban taba tunanin zan sake yin farin ciki ba, kuma duk a halin da na ga mijina ina son shi a haka.
"Sun kore shi daga aiki, ko suna tunanin ba na son abu na ne? Wallahi ina son shi, hakan da suka yi Allah ya sa hakan ne mafi alkairi."

Hussaina Iliya ta kuma yi godiya ga 'yar gwagwarmaya, Fauziyya D. Sulaiman da ta taimaka wajen tara mata kudi har Naira miliyan 2.1.

Kara karanta wannan

Talauci: Gwamnati ta kara ba yan kasa hakuri, Minista ya ce sauki na tafe

Duba bidiyon a kasa:

DHQ ta magantu kan tsare Seaman Abbas

Tun da fari, mun ruwaito cewa hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta ce za ta binciki batun tsare Seaman Abbas Haruna na tsawon shekaru shida da matarsa ta yi zargi.

Amma hedikwatar ta ba da tabbacin cewa babu wanda ya tsare jami'in sojan kamar yadda ake zargi kuma za a sanar da 'yan kasa sakamakon binciken da aka gudanar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.