Gangamin Zanga Zangar 1 ga Oktoba Ya Kankama, An Mika Bukatu ga Tinubu

Gangamin Zanga Zangar 1 ga Oktoba Ya Kankama, An Mika Bukatu ga Tinubu

  • Matasan kasar nan sun nuna rashin gamsuwa da salon tafiyar da tattalin arzikin Najeriya a mulkin Bola Tinubu
  • Ana shirin fita zanga-zanga a ranar 1 Oktoba, 2024 domin nunawa shugaba Bola Tinubu halin da ake ciki a yau
  • Daga cikin shirin da ake yi, an fitar da jerin bukatu ga gwamnatin tarayya da ake sa ran samunsu zai kawo sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Masu shirya zanga-zangar ranar 1 Oktoba, 2024 na matsa kaimi wajen tattaro kawunan matasan kasar nan domin nuna adawa da yadda ake tafiyar da gwamnati.

Masu fafutukar karkashin jagorancin shugaban Education Rights Campaign, Hassan Soweto sun ce akwai bukatar mazauna kasar nan su fito don bayyana halin da su ke ciki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware N24bn domin ragewa talakawa radadi, an fadi yadda tsarin yake

Bola Tinubu
Matasa sun mika bukatu ga gwamnati gabanin zanga zanga Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Hassan Soweto ya ce dole sai gwamnatin Bola Tinubu ta biya wasu bukatun yan kasar nan domin yayyafawa fushinsu ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga Zanga: Bukatun matasa ga Tinubu

Matasan kasar nan sun bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya daina amfani da manufofin bankin lamuni na duniya (IMF) wajen muzgunawa yan Najeriya.

Sauran bukatun sun hada da rage farashin litar fetur da na kudin wutar lantarki, gyara matatun fetur da gwamnati ta mallaka da sakin wasu masu fafutuka da yan jarida da gwamnati ta kama.

Wasu matasan Kano na goyon bayan zanga zanga

Kungiyar kare hakkin dan Adam da yaki da rashin adalci ta shaidawa Legit cewa ta na goyon bayan a nunawa gwamnatin kasar nan illar matakan da ta ke dauka.

Shugaban kungiyar, Umar Ibrahim Umar ya ce a baya da aka yi zanga-zanga, gwamnati ta shafawa idonta toka wajen kara farashin fetur.

Kara karanta wannan

Ranar 'yanci: Gwamnatin Tinubu ta lissafa muhimman ayyukan da ta yiwa talakawa

Matashin ya ce duk da koken yan kasa, gwamnatin tarayya ba ta tausayawa jama'a, ba, inda ya ce su na duba yiwuwar shiga zanga-zangar.

Kungiyoyi za su yi wa Tinubu zanga zanga

A baya mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago na duniya sun bayyana takaicin yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke kokarin dakile kungiyoyin kwadago daga hakkinsu a kasar.

An samu labarin cewa kama shugaban NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero da gwamnati ta yi ya fusata kungiyoyin, saboda haka ake shirin zanga-zanga a kasashen duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.