Mutuwa Ta Shiga Gidan Gwamnati: Uwar Gidan Gwamna Eno Ta Rasu a Asibiti

Mutuwa Ta Shiga Gidan Gwamnati: Uwar Gidan Gwamna Eno Ta Rasu a Asibiti

  • Allah ya karbi rayuwar uwar gidan gwamnan Akwa Ibom, Fasto Misis Patience Umo Eno a wani asibiti bayan fama da rashin lafiya
  • Kwamishinan yada labarai, Mista Ini Ememobong ya fitar da sanarwar rasuwar inda ya ce ta rasu ne a ranar Alhamis, 26 ga Satumba
  • Duk da rasuwar matarsa, sanarwar ta ce Gwamna Umo Eno ya ba al'ummar Akwa Ibom tabbacin jajircerwarsa wajen yi masu hidima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Akwa Ibom - Rahotannin da muka samu na nuni da cewa uwar gidan gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Misis Patience Umo Eno, ta rigamu gidan gaskiya.

An rahoto cewa Misis Patience Umo Eno ta amsa kiran mahaliccinta ne a ranar Alhamis a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Kara karanta wannan

Litar fetur ta koma N2500 bayan an fusata 'yan kasuwa, gwamnati ta dauki mataki

Uwar gidan gwamnan jihar Akwa Ibom ta rasu
Mai dakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno ta rasu. Hoto: @aksgovt
Asali: Twitter

Matar gwamnan Akwa Ibom ta rasu

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin X ta nuna cewa Uwargidan gwamnan ta rasu bayan ta yi fama da rashin lafiya kuma ta koma ga Ubangiji a yayin da ta ke tare da iyalanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, Mista Ini Ememobong ta ce iyalan gwamnan sun bukaci a basu sarari yayin da suke makokin Misis Patience.

Duk da rasuwar matarsa, Gwamna Umo Eno ya tabbatar wa mutanen Akwa Ibom cewa zai ci gaba da jajircewa wajen yiwa jihar hidima.

Za a fitar da karin bayani

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, sanarwar ta bayyana cewa:

“A cikin alhini ne muke sanar da rasuwar matar gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Patience Umo Eno, bayan rashin lafiya.
“Ta rasu a ne a wani asibiti a ranar 26 ga Satumba, 2024 a gaban danginta. Iyalinta na mika lamuransu ga Ubangiji tare da neman addu'a a wannan mawuyacin hali."

Kara karanta wannan

Majalisa ta yiwa Tinubu gata, ta amince da nadin sabuwar kwamishiniya a NPC

Sanarwar ta ce "za a fitar da karin bayani" nan da wani lokaci yayin da ya ke nuna godiyar Gwamna Umo Eno ga wadanda suka "kasance tare da iyalinsa a wannan lokacin".

Duba sanarwar a kasa:

Rukayat: Mawakiyar Musulunci ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar shahararriyar mawakiyar begen Annabi da harshen Yarbanci, Rukayat Gawat.

Da sanyin safiyar ranar Talata, 24 ga Satumba, 2024, aka fitar da labarin mutuwar tauraruwar mawakiyar tare da karin bayani kan lokacin jana'izarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.