Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da wasu Manyan Jami’an Gidan Yari 4, Ta Fadi Dalili

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da wasu Manyan Jami’an Gidan Yari 4, Ta Fadi Dalili

  • Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta dakatar da wasu jami'anta bisa zarginsu da karbar cin hanci da rashawa
  • A ranar Alhamis ne hukumar ta fitar da sanarwar dakatarwar inda ta ce ta dauki matakin ne domin ba ta damar gudanar da sahihin bincike
  • An ce gwamnati ta soma binciken ne bayan Idris Okuneye watau Bobrisky ya zargi jami'an hukumar da karbar masa miliyoyin Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami'an hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya bisa zargin su da hannu a karbar rashawa.

Idan ba a manta ba, an rahoto cewa fitaccen dan daudu, Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky ya zargi jami'an gidan yarin da karbar N15m daga wajensa.

Kara karanta wannan

Talauci: Gwamnati ta kara ba yan kasa hakuri, Minista ya ce sauki na tafe

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami'an hukumar gidan yari
Gwamnatin tarayya ta dakatar da jami'an hukumar gidan yari 4 kan zargin rashawa. Hoto: @CorrectionsNg
Asali: Twitter

Rahoton Channels TV ya nuna cewa gwamnatin tarayyar ta dakatar da jami'an gidan yarin bayan wani mawallafi, Martins Otse da aka fi sani da VeryDarkMan ya saki bidiyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin ma'aikata da karbar rashawa

A bidiyon, ya bayyana cewa Bobrisky ya sanar da shi yadda wasu jami'an hukumar EFCC suka karbi N15m daga hannunsa lokacin da aka kai shi gidan yari kan watsa Naira.

VeryDarkMan ya kuma yi ikirarin cewa Bobrisky ya biya miliyoyin Naira domin a ba shi wani kebantaccen daki a cikin gidan yarin.

To sai dai kuma tuni Bobrisky ya fito ya karyata wannan ikirari na VDM. Duk da haka, hukumar EFCC da ta gidajen yari sun kaddamar da bincike kan lamarin.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar gidajen gyaran hali ta kasa ta sanar da cewa ta dakatar da jami'an bayan nazartar zargin da aka yi masu a cikin bidiyon.

Kara karanta wannan

Bobrisky: Bayan korafin dan daudu, Gwamnati ta fara binciken shugaban gidajen yari

An dakatar da jami'an gidan yari

Sanarwar mai dauke da sa hannun Ja'afaru Ahmed ta ce an dakatar da jami'an domin ba hukumar damar gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masu, in Punch.

Jami'an da aka dakatar su ne; Michael Anugwa (DCC) mai kula da matsakaiciyar cibiyar tsaro da ke a Kirikiri, Legas da Sikiru Adekunle (DCC) da ke kula da babbar cibiyar tsaro (MSCC) a Kirikiri, Legas.
Sauran sun hada da; ASC II Ogbule Samuel Obinna, da ke aiki a cibiyar tsaro ta MSCC, Afikpo, jihar Ebonyi bisa zargin ya fitar da wani fursuna zuwa wajen cibiyar ba bisa ka'ida ba.
"Hukumar ta kuma dakatar da wani babban jami'i, Iloafonsi Kevin Ikechukwu (DCC) da ke kula da cibiyar tsaro ta MSCC, Kuje, Abuja bisa zargin karbar kudi a madadin fursunoni."

- A cewar sanarwar.

Za a binciki badakalar Bobrisky a gidan yari

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan ikirarin da dan daudu, Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky ya yi.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su wataya: Tinubu ya sanya ranar fara biyan sabon albashin N70000

Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya umarci fara bincike kan zargin cin hanci a gidan yari bayan dan daudu ya zargi jami'an hukumar da karbar miliyoyinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.