Majalisa Ta Gaji, Ta Tsoma Baki a Dambarwar Kamfanin NNPCL da Matatar Dangote

Majalisa Ta Gaji, Ta Tsoma Baki a Dambarwar Kamfanin NNPCL da Matatar Dangote

  • Majalisar wakilai ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya sa baki kan dambarwar dakon fetur kai tsaye daga matatar Dangote
  • Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta zargi kamfanin NNPCL da haramta ma ta dakon fetur kai tsaye daga matatar Dangote
  • Amma a kudirin da ya gabatar, 'Dan Majalisa mai wakiltar Yenagoa/Opokuma a Beyelsa, Oboku Oforji ya ce a sake duba batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Majalisar wakilan kasar nan ta shawarci gwamnatin tarayya ta umarci NNPCL ya sahalewa yan kasuwa su fara sayo fetur kai tsaye daga matatar Dangote.

Wannan na zuwa a sa'ilin da ake samun dambarwa tsakanin dillalan man fetur da Dangote a gefe guda, kamfanin mai na kasa (NNPCL) a daya gefen.

Kara karanta wannan

"Sai ka gurfana a gaban kotu:" Hukumar EFCC ta kalubalanci Yahaya Bello

NNPCL
Majalisa ta nemi a kyale yan kasuwa su sayo fetur daga Dangote Hoto: Abbas Tajuddeen
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kiran ya biyo kudirin gaggawa da Dan Majalisa mai wakiltar Yenagoa/Opokuma a jihar Beyelsa, Oboku Oforji ya gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Dangote: Majalisa ta goyi bayan yan kasuwa

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa a bayaninsa, Dan Majalisa Oboku Oforji ya koka kan yadda ake han yan kasuwa sayo fetur daga matatar Dangote ke tacewa.

Ya ce tun da matatar ta fara aiki a ranar 15 Satumba, 2024 ta na tace ganga 6,500 a kullum, amma NNPCL na barin zababbun manyan yan kasuwa ne kawai su yi dakon man.

NNPCL vs Dangote: Majalisa ta hango matsala

Majalisar wakilai ta ce matukar ba a ba sauran yan kasuwar fetur damar dakon mai kai tsaye daga Dangote ba, yan kasar nan za su cigaba da shan wahalar fetur.

Ya koka kan yadda matsawar da NNPCL ta yi ke kokarin tura kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) shigo da fetur da kansu daga kasashen waje.

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

An gano illar sayo fetur daga Dangote

A wani labarin kun ji cewa kungiyar manyan ma'aikatan fetur da gas (PENGASSAN) ta ce yan kasuwa ba za su iya dauko fetur daga matatar Dangote ba.

Shugaban kungiyar, Festus Osifo ne ya fadi haka, inda ya ce kamfanin NNPCL kan sayo da tsada, sannan ya sayarwa yan kasuwar kasar nan da sauki domin a sayar da dama-dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.