Ma'aikata Sun Cika da Murna: Gwamna Zai Fara Biyan Sabon Albashin N70000 a Oktoba
- Gwamna Chukwuma Soludo ya sanar da cewa zai fara biyan ma'aikatan jiharsa ta Anambra sabon albashin N70,0000 a watan Oktoba
- Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da dukkanin shugabannin makarantun firamare da sakandare na jihar a Awka
- Hakazalika, Soludo ya sanar da fara aiwatar da tsarin ilimi kyauta ga manyan daliban sakandare a makarantun gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa jiharsa ta shirya fara biyan sabon mafi karancin albashi.
Gwamna Chukwuma Soludo ya ba ma'aikatan jiharsa tabbacin cewa daga watan Oktobar 2024 za su fara karbar albashin N70,000.
Gwamna zai fara biyan sabon albashi
Soludo ya bayyana hakan ne a cibiyar bunkasa mata ta Farfesa Dora Akunyili da ke Awka a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi albishir din ne a lokacin da ya ke ganawa da shugabanni makarantun firamare da sakandare na gwamnati da ke a fadin jihar.
“Jihar Anambra za ta fara biyan mafi karancin albashi na N70,000 daga wata mai zuwa."
- A cewar gwamnan Anambra.
Gwamna ya kawo tsarin ilimi kyauta
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, daga mako mai zuwa, za a samar da tsarin ilimi kyauta ga manyan dalibai a dukkanin makarantun gwamnati a jihar.
The Nation ta ruwaito Sulodo ya kuma ba da umarnin a mayar wa daliban da suka rigaya suka biya N5,000 na wannan zangon karatun kudinsu yana mai cewa:
"Daga mako mai zuwa, za a samar da tsarin ilimi kyauta ga manyan dalibai a duk makarantun gwamnati na gwamnatin jihar Anambra."
A shekarar 2023, gwamnatin Anambra tafara aiwatar da tsarin ilimi kyauta ga 'yan firamare da kuma daliban sakandare na aji daya zuwa uku a dukkanin makarantun gwamnatin jihar.
Tinubu zai fara biyan sabon albashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu ta ce za ta fara aiwatar da biyan sabon albashin N70,000 daga Yulin 2024.
Hakazalika, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta amince da sake tsarin albashin wasu ma'aikata da suka hada da liktoci, malamai da sauransu.
Asali: Legit.ng