Tsohon Dan Majalisa Ya Ba Gwamna Dauda Lakanin Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Zamfara
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu shawara kan matsalar rashin tsaron da ta daɗe tana addabar al'umma
- Wani tsohon ɗan majalisar wakilai ya buƙaci gwamnan ya daina ɗora alhaki kan wasu dangane da matsalar ƴan bindiga
- Hon. Sani Takori wanda tsohon Antoni Janar na jihar ne ya buƙaci Gwamna Dauda da ya haɗa kai da gwamnatin tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Tsohon ɗan majalisar wakilai, Sani Takori, ya ba gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, shawara kan matsalar rashin tsaro.
Sani Takori ya buƙaci Gwamna Dauda ya da daina ɗora alhaki kan wasu dangane da matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar.
Wace shawara aka ba Gwamna Dauda?
Tsohon ɗan majalisar ya buƙaci gwamnan da ya maida hankali wajen haɗa kai da gwamnatin tarayya domin magance matsalar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Sani Takori ya nuna damuwarsa kan cacakar bakin da ake yi tsakanin Gwamna Dauda Lawal da ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle.
Ya yi nuni da cewa maimakon su duka biyun sun haɗa kansu domin magance matsalar ƴan bindiga, sun koma yin cacar baki a kafafen yaɗa labarai.
"Idan ku duka biyun kuka haɗa kanku, za ku samu nasara kan waɗannan miyagun da suka lalata rayuka da dukiyoyi tare da ƙara talautar da mutanen mu."
- Sani Takori
Ya ƙara da cewa duk da bambancin siyasa da ke tsakaninsu, ya kamata ta'asar da ƴan bindiga ke yi ta tilasta musu haɗa kai domin kawar da su ta yadda za a kare rayukan bayin Allah.
Ƙungiya ta fallasa Gwamna Dauda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya mai suna Northern Youths Awareness (NYA) ta yi magana kan taƙaddamar gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da Bello Matawalle.
Ƙungiyar ta yi iƙirarin cewa Gwamna Dauda Lawal, yana jin tsoron ƙaramin ministan tsaron ne saboda batun babban zaɓen 2027 da ke tafe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng