Zargin $49bn: Jonathan Ya Maidawa Sanusi II Martani kan Satar Kudi a Gwamnatinsa
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya karyata labarin batan Dala biliyan 49 a gwamnatinsa a shekarun baya
- Shugaban ya ce babu yadda za a yi irin wannan makudan Daloli su bata, amma gwamnatin kasar nan ba za ta girgiza ba
- Dr. Jonathan ya yi bayani kan abin da ya faru tsakanin gwamnatinsa da tsohon gwamnan CBN, Sanusi Lamido Sanusi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi karin haske kan zargin batan Dala biliyan 49 daga asusun gwamnatin tarayya a zamaninsa.
Tsohon shugaban ya bayyana haka ne yayin taron kaddamar da littafi da aka rubuta a kan gudanar da shugabancin jama'a.
Goodluck Jonathan ya ce $49 bai bace ba
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Jonathan ya karyata labarin da ke cewa Dalolin sun yi batan dabo a karkashin gwamnatinsa, kamar yadda aka rika yayatawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi wa littafin suna da ‘Public Policy And Agents’ Interests: Perspectives From The Emerging World’.
CBN: Jonathan ya musanta korar Sarki Sanusi
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya musanta cewa ya kori tsohon gwamnan babban bankin kasa kuma sarkin Kano na 16, Malam Muhammad Sanusi II.
Tsohon shugaban kara da cewa abubuwan da ke kunshe a littafin bai kwanta masa ba, domin babu gaskiya kan zargin batan kudi a mulkinsa.
Jonathan ya yi bayanin 'batan daloli'
Dr. Jonathan ya bayyana cewa a wancan lokaci da gwamnan CBN ya yi zargin batan makudan kudi daga asusun gwamnati, an dauki matakin dakatar da Sanusi Lamido Sanusi ne.
Ya ce babu ta yadda irin wannan kudi za su bace daga asusun gwamnati ba tare da yan kasa sun girgiza da lamarin da ya afku ba.
Jonathan ya fadi mafitar magudin zabe
A wani labarin kun ji cewa tsohon shugaban kasar nan, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana sahihiyar hanyar da za a magance magudin zabe da ke damun siyasar kasar nan.
Tsohon shugaban wanda ya bayyana takaicin yadda magudi ya samu wurin zama a dimukuradiyyar Najeriya, ya ce amfani da kimiyya da fasaha kawai mafita.
Asali: Legit.ng