Edo: Jonathan Ya Fadi Hanyar da za a Magance Maguɗin Zabe a Najeriya

Edo: Jonathan Ya Fadi Hanyar da za a Magance Maguɗin Zabe a Najeriya

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi magana kan zaben gwamna da ya gabata a jihar Edo ranar Asabar
  • Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa amfani da kimiyya da fasaha kawai ba za ta magance matsalolin maguɗin a zabe ba
  • Haka zalika shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana babban abin da ya tsaya masa a rai kan harkokin mulki a tarayyar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugabanni da masana na cigaba da sharhi kan yadda zaben gwamna ya gudana a jihar Edo ranar Asabar.

Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya koka kan yadda ake samun maguɗin zabe har yanzu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya fara rabawa waɗanda ambaliya ta shafa kuɗi da kayan abinci

Jonathan
Jonathan ya yi magana kan magudin zabe. Hoto: Goodluck Ebele Jonathan
Asali: Getty Images

Jaridar This Day ta wallafa cewa shugaba Jonathan ya yi bayanin ne yayin wani taron zaman lafiya a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyar magance maguɗin zabe a Najeriya

Arise News ta wallafa cewa shugaba Goodluck Jonathan ya ce mutane na yawan bayani kan amfani da fasahar zamani wajen magance maguɗin zabe amma ba haka ba ne mafita.

Goodluck Jonathan ya ce idan ana son kawo karshen maguɗin zabe dole sai mutane sun canza halayensu, musamman yan siyasa.

Ya kara da cewa ko da za a samar da na'urori amma idan halin mutane ba kyau, za su yi maguɗi da na'urorin.

Abin da ya damu Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce abin da yake kawo tashin hankali a ƙasashe shi ne rashin shugabanci na gari.

Saboda haka ne shugaba Jonathan ya ce babban abin da ya dame shi a Najeriya shi ne gyaran harkar shugabanci.

Kara karanta wannan

'Matsalolin sun yi yawa,' Za a yi taro domin tunkarar Tinubu da murya 1

Jonathan da bukatar zaman lafiya a Afrika

Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga yan Afrika kan muhimmacin koyar da zaman lafiya da yin abubuwan da za su kawo zaman lafiya.

Jonathan ya ce yana da muhimmanci sosai yunkurin samar da zaman lafiya ya zama yana samuwa a ko da yaushe a Afrika.

Kungiyoyi sun kushe zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa wasu kungiyoyi da suka saka ido a zaben Edo sun fitar da rahoto kan yadda zaben ya gudana da yadda aka tatttara kuri'u

Kungiyoyin sun ce zaben bai cika sharudan ingantaccen zabe ba kuma sun zargi hukumar INEC da karya dokokin zaɓe na kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng