Gwamna a Arewa Ya Haramta Noma a Wurare 2 bayan Makiyaya Sun Kai Ƙorafi
- Gwamnatin Katsina karkashin Gwamna Dikko Radda ta haramta noma a labi da sauran filayen kiwo a faɗin kannanan hukumomi
- Sakataren gwamnatin Katsina, Abdullahi Garba Faskari ne ya bayyana haka yayin da je duba halin da ake ciki a Mai'adua da Zango
- Ya ce an yi zama tsakanin makiyaya da manoma kuma sun cimma matsayar ba za a sake noma a labin da shanu ke bi suna wucewa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnatin Katsina ta haramta noma a kan labi ma'ana hanyoyin shanu da filayen kiwo a jihar daga karshen daminar bana 2024.
Sakataren gwamnatin jiha (SSG), Alhaji Abdullahi Garba Faskari ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Mai’adua da Zango don duba halin da ake ciki.
Dalilin gwamnatin Kastina na ɗaukar mataki
Ya ce gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin kawo karshen saɓanin da ke haddasa rigima tsakanin manoma da makiyaya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdullahi Faskari ya ce ya kawo ziyara ne bayan samun rahoto daga makiyaya cewa an yi noma a hanyar da suke wucewa da shanu a wasu ƙananan hukumomi.
Ya ce gwamnatin Katsina ta zauna da makiyaya da manoman da abin ya shafa kan lamarin musamman dangane da wani labi da ya tafi har zuwa Jamhuriyar Nijar.
Katsina: Manoma da makiyaya sun cimma matsaya
"Mun gayyaci makiyaya da manoma tare da shugaban karamar hukumar domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
"An yi yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu cewa za a girbe amfanin gona da aka noma a kan hanyoyin shanu, amma wannan shi ne noma na ƙarshe a hanyoyin.
“Tawagar ta ziyarci Mai’adua kuma ta tabbatar da yarjejeniyar. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da, Mashi, Kaita, Dutsinma, Mai’adua da Zango."
- Abdullahi Garba Faskari.
Sakataren gwamnatin Katsina ya tabbatar da cewa daga yanzu an hana noma a kan labi, wuraren da shanu ke wucewa da filayen kiwo, rahoton Punch.
Manoma sun ba gwmanati shawara
Wani manomi a Katsina, Malam Bello Sagir, ya faɗa mana cewa wannan mataki ne mai kyau amma ya kamata gwamnati ta ja kunnen makiyaya su daina shiga gonaki.
Da yake hira da wakilin Legit Hausa, Bello ya ce idan an hana manoma taɓa wuraren da aka warewa fulani, to ya kamata makiyayan su tsaya iya inda aka ajiye su.
Manomin ya ce:
"Wannan mataki ne mai kyau, manoma su daina taɓa wuraren da aka ware domin kiwo, haka su ma fulani su kula da shanunsu, su daina shiga suna ɓarna a gonaki.
"Ka san na taɓa shiga rigima da makiyaya a baya saboda sun cinye mun amfanin noma, duk da haka na san muna masu laifi, amma ya kamata su riƙa kiyaye wa.
"Yanzu kamar yadda gwamnati ta yi wannan dokar to ta tabbatar ana bi, sannan ta ja kunnen fulani su tsaya iyakarsu, idan aka yi haka tabbas za a zauna lafiya."
Katsina ta ware wa aikin ruwa N22bn
Kuna da labarin gwamnatin Katsina ta ware kuɗi N22bn domin aikin samar da wadataccen ruwan sha a faɗin kananan hukumomi 34.
Shugaban hukumar ruwa ta Katsina, Tukur Hassan ne ya bayyana hakan, ya ce aikin zai kawo ƙarshen ƙarancin ruwa da rashin tsaftarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng