"Sai an Sake Zama:" Sanatan APC Ya Nemi Tinubu Ya Kira Taron Gaggawa kan Tattali

"Sai an Sake Zama:" Sanatan APC Ya Nemi Tinubu Ya Kira Taron Gaggawa kan Tattali

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu shawara kan tattalin arzikin kasar nan
  • Sanatan ya ce duk da akwai bukatar cire tallafin man fetur, amma an jefa yan kasa cikin wahala sosai
  • Tsohon gwamnan Abia ya nemi a gaggauta kiran taron masu ruwa da tsaki domin nemo hanyar taimakon jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu ya shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kira taron gaggawa da masu ruwa tsaki.

Sanatan na Arewacin Abia ya na ganin akwai bukatar haka a yanzu duba da matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan.

Kara karanta wannan

"Sai ka gurfana a gaban kotu:" Hukumar EFCC ta kalubalanci Yahaya Bello

Orji Kalu
Sanata ya shawarci Tinubu kan tattalin arziki Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa, Sanata Kalu wanda ke a matsayin shugaban kwamitin sayar da kadarorin gwamnati ya ce kasar nan na cikin wani hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu ya kira taron gaggawa:" Sanata

Arise News ta wallafa cewa Sanata Kalu ya ce cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi lokaci guda ya kuntata wa jama'ar kasar nan matuka.

Amma ya yi gaggawar kare gwamnati, inda y kara da cewa wannan shi ne tsarin da ya dace a tafi a kai, sai dai ana bukatar zaman gaggawa domin duba wahalar da ake ciki.

"Tinubu zai iya kawo sauki," cewar Sanata Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce duk inda ya shiga a jiharsa ba abin da ya ke karo da shi sai kuncin rayuwa da jama'a ke ciki.

Sanatan ya ce sai dai shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai iya magance matsalar ta hanyar zaman gaggawa da wanda su ka dace don duba batun.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya gaji da matsin lambar EFCC, ya roƙi Tinubu Alfarma

"Afrika na da arziki," cewar Tinubu

A baya kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce nahiyar Afrika na cike da albarkatun kasa wanda duniya ke bukata domin cigabanta.

Shugaban, wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta a taron Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada bukatar ba nahiyar hadin kai domin ciyar da al'umarta gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.