NYSC: Matasa Ƴan Bautar Ƙasa Za Su Warwasa, An Ƙara Masu Alawus Duk Wata
- Gwamnatin Najeriya ta ƙara alawus da ake biyan masu yi wa kasa hidima kowane wata daga N33,000 zuwa N77,000
- Legit Hausa ta fahimci wannan ƙarin ya yi daidai da dokar sabon mafi karancin albashi da aka yi wa garambawul 2024
- Hukumar NYSC ta ce ƙarin zai taimakawa matasan tare da zaburar da su domin su ƙara dagewa wajen yi wa ƙasa hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da karawa matasa masu yi wa ƙasa hidima alawus-alawus da ake biyansu duk wata daga N33,000 zuwa N77,000.
Wannan ƙarin na alawi da gwamnati ta yi wa ƴan bautar ƙasa ya fara aiki ne daga watan Yuli, 2024.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar kula da ƴan bautar kasa watau NYSC ta wallafa a shafinta na manhajar X ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NYSC: An kara alawi zuwa N77,000
Ta ce wannan ƙarin ya biyo bayan zartar da dokar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 wanda gwamnatin tarayya da ƴan kwadago suka amince da shi.
Sanarwar ta ce:
"Gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin alawus na wata-wata da ake biyan matasa ƴan bautar ƙasa zuwa N77,000 daga watan Yulin 2024.
"Hakan ta faru ne sakamakon aiwatar da dokar sabon mafi ƙarancin albashi ta 2024."
- NYSC
Hukumar NYSC ta ƙara da cewa shugaban hukumar kula da albashin ma'aikata ta ƙasa, Mr. Ekpo Nta ne ya tabbatar da haka a wata wasiƙa da ya aiko ranar 25 ga watan Satumba.
Hukumar NYSC ta godewa gwamnatin tarayya
Shugaban NYSC na ƙasa, Birgediya Janar YD Ahmed ya yabawa gwamnatin tarayya bisa wannan ƙari da ta yiwa ƴan bautar ƙasa wanda ya zo a lokacin da ya dace.
Ya kuma bayyana kwarin guiwar cewa ƙarin zai ƙara zaburar da ƴan bautar ƙasa su ƙara kaimi wajen yi wa ƙasarsu hidima.
Idan ba ku manta ba a kwanakin baya shugaban NYSC ya ziyarci hukumar albashi ta ƙara, inda ya roƙi a ƙara inganta walwalar masu yi wa ƙasa hidima.
Ɗiyar gwamna ta sha wuya a sansanin NYSC
A wani rahoton gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana yadda ƴarsa ta sha wahala a sansanin horas da matasa masu bautar ƙasa.
Seyi Makinde ya ce ya yi mamaki yadda ta iya shafe makwanni uku bayan ta ce masa kwana ɗaya kawai za ta yi sansanin ta fito.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng