‘Abin da Ya Sa Tinubu ba Zai Tsoma Baki a Rigimar NNPCL da Dangote ba’

‘Abin da Ya Sa Tinubu ba Zai Tsoma Baki a Rigimar NNPCL da Dangote ba’

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi magana kan rigimar da ke faruwa tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Aliko Dangote
  • Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ba zai tsoma baki kan rigimar da ke faruwa tsakaninsu ba saboda suna cin gashin kansu
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka fara takun-saka tsakanin kamfanonin guda biyu tun bayan Dangote ya fara fitar da mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi magana kan rigima tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Aliko Dangote.

Gwamnatin ta ce Shugaba Bola Tinubu ba zai shiga lamarin rigima tsakanin kamfanonin guda biyu ba.

Tinubu ya magantu kan rigimar Dangote da kamfanin NNPCL
Shugaba Bola Tinubu ya ce bai zai tsoma baki a rigimar matatar Dangote da NNPCL ba. Hoto: Nigeria National Petroleum Corporation.
Asali: UGC

Tinubu ya magantu kan rigimar Dangote, NNPCL

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

Hadimin shugaban kasa a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga shi ya bayyana haka a yau Laraba 25 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya ce dukkan bangarorin guda biyu suna aiwatar da ayyukansu ne daban-daban musamman a harkokin kasuwancinsu.

Ya ce duk da dokar kamfanoni na man fetur (PIA), NNPCL ya na da yanci duk da kasancewarsa ta gwamnati, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Dalilin Tinubu na kin shiga rigimar NNPCL-Dangote

"Duk wata matsala da kamfanonin biyu ke da su ya rage na su saboda matatar Dangote tana zaman kanta ne."
"Duba da dokar PIA na kamfanonin mai, NNPCL yana zaman kanta ne duk da kasacewarsa mallakin gwamnati."
"Abokan hulda ne za su ci moriya lokacin da aka fara samun rigima kan farashin fetur, idan man NNPCL ya yi tsada, yan kasuwa za su iya kawo na su tare da yi masa farashi yadda suka ga ya kamata."

Kara karanta wannan

Bayan fara aikin matatarsa: Dangote ya samu kwangilar N158bn daga gwamnatin Tinubu

- Cewar sanarwar

Dangote ya magantu kan cire tallafin mai

Kun ji cewa attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya yi magana kan cire tallafin man fetur inda ya ba Bola Tinubu shawara

Dangote ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta cire maganar biyan tallafin man fetur gaba daya domin daidaita lamura.

Hakan ya biyo bayan korafe-korafe da ake ta yi bayan cire tallafin man fetur da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.