Matatar Dangote: Malamin Addini Ya Ba Gwamnatin Tarayya Lakanin Yadda Fetur Zai Yi Arha
- Rabaran Gabriel Abegunrin ya ba gwamnatin tarayya kan matatar Dangote da ke Lekki a jihar Legas da ke Kudancin Najeriya
- Babban limamin na cocin Katolika da ke Ibadan ya buƙaci gwamnati ta bari Dangote ya riƙa saida fetur kai tsaye ga ƴan kasuwa
- Malamin addinin ya yi nuni da cewa idan aka yi hakan za a samu arhar man fetur ta yadda ƴan Najeriya za su siya da sauƙi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Babban limamin cocin Katolika na Ibadan Archdiocese, Rabaran Gabriel Abegunrin, ya ba gwamnatin tarayya shawara kan matatar Dangote.
Malamin addinin ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta bar matatar Dangote ta sayar da man fetur ga ƴan kasuwa kai tsaye.
Wace shawara malamin ya ba da kan Dangote?
Rabaran Gabriel ya bayyana hakan ne a ranar Larabar a birnin Ibadan a wani taron manema labarai da cocin ta shirya domin bikin cikarsa shekara 75 da haihuwa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabaran Gabriel Abegunrin ya ce barin Dangote ya yanke farashin fetur da sayarwa ƴan kasuwa kai tsaye zai sa mutane su samu sauƙi da arha maimakon ta hannun kamfanin mai na ƙasa (NNPCL).
Malamin addinin ya kuma buƙaci gwamnatoci a dukkan matakai da su ci gaba da yin bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rabaran ya ba matasa shawara
Rabaran Abegunrin ya buƙaci matasa da su gyara ɗabi'unsu, su gujewa duk wani nau’i na munanan ɗabi’u da kuma yin sana’o’in dogaro da kai.
"Ba gaskiya ba ne cewa babu aikin yi, matasa za su iya amfani da hannayensu domin yin aiki, za su iya yin noma su kafa kansu."
"Muna kuma kira ga duk masu kishin ƙasa da su ƙarfafawa matasa gwiwa, a samar musu ayyukan yi tare da ba su shawarwari yadda ya kamata."
- Rabaran Gabriel Abegunrin
NNPCL ya fadi dalilin hana sayan fetur na Dangote
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya bayyana cewa ƴan kasuwa ba za su iya shigo da mai ko sayen shi daga matatar Dangote ba.
NNPCL ya sanar da cewa har yanzu farashin man Dangote bai daidaita ba kuma man bai kai ga wadatar da zai sa har 'yan kasuwa su fara saya ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng