An Saka Sarki Sanusi II a Gaba kan Zargin Rashin Girmama Annabi Muhammad SAW
- Al'ummar Arewacin Najeriya na cigaba da yin fashin baki kan wata darduma da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya saka a fadarsa
- Mutane da dama a kafafen sadarwa har da malaman addinin Musulunci suna ganin bai kamata sarkin ya yi amfani da dardumar ba
- Legit ta gano cewa a jikin dardumar an rubuta cikakken sunansa wanda akwai "Muhammadu' a ciki kuma hakan ne ya jawo surutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Amfani da darduma mai dauke da sunan 'Muhammadu' a fadar sarkin Kano ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sadarwa.
Yan Najeriya masu amfani da kafafen sadarwa sun yi kira ga sarkin kan cire dardumar ko kuma cire sunan 'Muhammadu' a jikinta.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa wani malamin addinin Musulunci a Zariya, Muhammad Sharif ya yi zazzafan martani ga sarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dardumar Sanusi II da ta jawo magana
Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana da darduma mai dauke da rubutun 'Khalifa Muhammadu Sanusi II'.
An fara magana kan dardumar ne bisa zargin cewa sarkin yana taka ta kuma tana dauke da sunan 'Muhammad', sunan Manzon Allah SAW wanda aka ce ya kamata ya girmama sunan.
Malaman addini sun saka Sanusi II a gaba
Wani malamin addinin Musulunci a Zariya, ya ce a matsayin Sanusi na Khalifan Tijjaniyya ya kamata ya girmama sunan 'Muhammadu' a fadarsa.
Malamin ya ce ya dace Sanusi II ya bi tafarki irin na shugabannin darikar Tijjaniyya wajen girmama sunan.
Haka zalika wani malamin Tijjaniyya, Ali Abdulrahman ya ce da a zamanin Imam Malik sarkin yake taka dardumar, da an yi masa horo.
Sanusi II ya maida raddi game da dardumar
Sai dai tun farkon ce-ce-ku-cen Muhammadu Sanusi ya warware zancen kan cewa mutane ne ba su fahimce shi ba.
Muhammadu Sanusi II ya ce a shirye yake a ajiye fahimtarsa idan aka kawo masa hujjoji gamsassu.
El-Rufa'i ya yi magana kan Sanusi II
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana jin dadinsa game da dawo da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Nasir El-Rufai wanda aminsa ne sosai, ya ce ya ji dadi matuka game da lamarin inda ya ce hakan na daga abin da ya fi faranta masa rai a rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng