Bayan Korafin Dan Daudu, Gwamnatin Tinubu Ta Fara Bincike kan Shugaban Gidajen Yari

Bayan Korafin Dan Daudu, Gwamnatin Tinubu Ta Fara Bincike kan Shugaban Gidajen Yari

  • Bayan fitar wata murya da daudu, Bobrisky ke zargin ba jami'an EFCC da na gidan yari cin hanci, an kafa kwamitin bincike
  • Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo shi ya ba da umarnin fara bincike kan zargin cin hanci da Idris Okuneye ya yi
  • Hakan ya biyo bayan yada muryar dan daudun da aka yi inda ya ce ya ba shugaban hukumar NCS, Haliru Nababa cin hanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya umarci fara bincike kan zargin cin hanci a gidan yari.

Ministan ya ba da umarnin yin bincike mai zurfi bayan zargin jami'an hukumar gidan yari da dan daudu, Idris Okuneye (Bobrisky) ya yi.

Kara karanta wannan

'Dan PDP ya fashe da kuka a bidiyo yayin hira a gidan talabijin kan zabe

Ministan Tinubu a umarci binciken cin hanci bayan zargin Bobrisky
Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya umarci kaddamar da bincike kan shugaban gidajen yari. Hoto: Ministry of Interio, Bobrisky.
Asali: Facebook

Bobrisky: An fara binciken shugaban gidajen yari

Daily Trust ta ruwaito cewa Ministan ya ba da umarnin ne ta bakin kakakinsa, Babatunde Alao a yau Laraba 25 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umarnin ya biyo bayan sakin wata murya da aka yi inda dan daudu, Bobrisky ya fadi yadda ya ba jami'an hukumar cin hanci da kuma EFCC.

Bobrisky a cikin muryar ya bayyana cewa ya ba jami'an hukumar EFCC N15m da kuma shugaban hukumar gidan yari, Haliru Nababa cin hanci.

Dan daudun ya ce ya yi hakan ne domin a rage masa yawan zamansa a gidan yari bayan garkame shi da aka yi.

Ministan ya yi Allah wadai da wannan hali da ake zargin jami'an hukumar inda ya bukaci yin binciken kwa-kwaf.

Tunji-Ojo ya ce ba zai taba lamuntar irin wannan hali ba inda ya ce za a ɗauki mummunan mataki bayan yin binciken.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige limamin masallaci har lahira a Abuja, sun sace mutum 1

Martanin Bobrisky kan muryar da ke yawo

Sai dai kuma a bangarensa, Bobrisky ya ƙaryata cewa ya fadi haka a muryar da ake haɗawa musamman a kafofin sadarwa, cewar rahoton Punch.

Har ila yau, hukumar EFCC ta gayyaci Bobrisky da VeryDarkMan da ya yada muryar zuwa ofishinta domin taimakonsu kan binciken.

Bobrisky ya nemi alfarmar kotu

Kun ji cewa dan daudu, Bobrisky ya bukaci kotun ta yi masa sassauci wurin sauya zaman gidan kaso zuwa kudi N200,000 domin ya biya.

Wannan na zuwa ne bayan alkalin kotun a jihar Legas, Abimbola Awogboro ya yanke masa hukunci kan cin mutuncin naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.