An Fara Bankaɗo ‘Laifuffukan’ Buhari, CBN Ya Zargi Tsohon Shugaba da Durƙusa Tattali
- Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Olayemi Cardoso ya yi magana kan matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a Najeriya
- Olayemi Cardoso ya ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tattalin arziki ne da ya riga ya ruguje kuma yana kan gyara ne a yanzu
- Gwamnan bankin ya bayyana cewa tun a shekarar 2015, farkon gwamnatin Muhammadu Buhari aka fara lalata tattalin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnan Bankin Najeriya (CBN) ya yi magana kan wasu tsare tsare da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo a Najeriya.
Olayemi Cardoso ya ce matsalolin tattalin arziki da aka shiga a Najeriya sun samo asali ne tun a shekarar 2015.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa gwamnan CBN ya ce a yanzu haka an dauko hanyar gyara kuma akwai haske a gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CBN: 'Buhari ya gadar da tattali mai rauni'
Gwamnan Babban Bankin Najeriya na CBN ya ce wahalar rayuwa da ake ciki ta samo asali ne saboda rashin kula da tattalin kasar daga 2015 zuwa 2023.
Olayemi Cardoso ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tattalin arzikin Najeriya ne a rikice amma a yanzu tana kokarin gyara.
Bankin CBN ya je Buhari ya buga kudi sosai
Olayemi Cardoso ya ce a lokacin da Buhari ya samu mulki a 2015, ruwan kudi a Najeriya kimanin Naira tiriliyan 19 ne.
Amma a cewarsa, daga 2015 zuwa 2023, an samu ruwan kudi da aka buga a Najeriya har Naira tiriliyan 54 wanda hakan ya jawo rikicewar tattali.
Ƙoƙarin CBN na farfaɗo da tattalin Najeriya
Gwamnan CBN ya ce a halin yanzu sun dauki matakai domin farfaɗo da tattalin Najeriya da daura ƙasar kan turba mai kyau.
Cardoso ya kuma tabbatar da cewa bisa alamun da suka fara gani akwai hasken cewa za a samu nasara.
CBN ya ce za a samu sauki a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya ce man feturin Ɗangote zai daidaita farashin sufuri da rage tsadar abinci a Najeriya.
Cardoso ya bayyana haka ne a Abuja ranar talata, 24 ga watan Satumba, 2024 jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin MPC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng