Majalisar Dattawa Ta Amince da Buƙatar Tinubu, Ta Tabbatar da Naɗin CJN a Najeriya
- Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta zama sabuwar shugabar alƙalan Najeriya watau CJN bayan tantancewa a majalisar dattawa
- Majalisar ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Tinubu, ta tabbatar da naɗin a zamanta na ranar Laraba, 25 ga watan Satumba 2024
- Tun a watan Agusta, Tinubu ya rantsar da Kudirat a matsayin muƙaddashin CJN bayan Mai Shari'a Ariwoola ya yi ritaya daga aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin alkalin alkalan Najeriya (CJN).
Tun a watan Agusta, Kudirat Kekere-Ekun ta zama muƙaddashiyar CJN bayan Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya daga aiki.
Daily Trust ta ce CJN ta samu rakiyar wasu alkalan kotun koli da na kotun daukaka kara zuwa zauren majalisar dattijai da karfe 12:30 na tsakar rana yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya aika saƙo majalisar dattawa
Wannan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya buƙaci majalisar dattawan ta tabbatar da naɗinta a wata wasika da ya aika jiya Talata.
Bayan karanta wasiƙar, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya miƙa bukatar ga kwamitin da ta kunshi dukkan sanatoci domin tantancewa ranar Laraba.
Bayan kammala tattaunawa da tantancewa, Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Kudirat Kekere-Ekun a matsayin sabuwar CJN a Najeriya.
Sabuwar CJN ta sha alwashin kawo sauyi
A yayin tantancewa a zauren majalisa, Mai shari’a Kekere-Ekun ta ce za ta yi amfani da fasahar zamani domin tabbatar an yi wa mutane adalci cikin ƙankanin lokaci.
Haka nan kuma ta bayyana cewa masu cin hanci da rashawa masu aikata miyagun laifuka sun shiga uku a hannun shari'a domin ba za su da wurin ɓuya.
Sabuwar CJN ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ɓangaren shari'a ya dogara da kansa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Rasuwar sanata ta hana zaman majalisa
Kun ji cewa Majalisar wakilai ta ɗage zamanta na farko bayan dawowa daga hutun shekara-shekara domin jimami da karrama marigayi Sanata Ifeanyi Ubah.
Sanatan mai wakiltar Anambra ta Kudu a majalksar dattawa ya riga mu gidan gaskiya ne a watan Yuli lokacin ƴan majalisa sun tafi hutu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng