El Rufai Ya Fadi Yadda Ya Ji bayan Dawo da Sanusi II Sarautar Kano da Aka Tuge a 2020

El Rufai Ya Fadi Yadda Ya Ji bayan Dawo da Sanusi II Sarautar Kano da Aka Tuge a 2020

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana jin dadinsa game da dawo da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
  • Malam El-Rufai ya ce ya ji dadi matuka game da lamarin inda ya ce hakan na daga abin da ya fi faranta masa rai a rayuwa
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya tuge Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kwanaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya yi magana kan dawowar Muhammadu Sanusi II sarauta.

Nasir El-Rufai ya ce dawo da Mai martaba Muhammadu Sanusi II kan sarauta na daya daga cikin abin da ya fi faranta masa rai a rayuwa.

Kara karanta wannan

An Saka Sarki Sanusi II a gaba kan zargin rashin girmama Annabi Muhammad SAW

El-Rufai ya yi farin ciki da dawowar Sanusi II sarauta
Nasir El-Rufai ya fadi yadda ya ji dadi bayan dawo da Sanusi II sarautar Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Nasir El-Rufai.
Asali: Facebook

El-Rufai ya ji dadin dawowar Sanusi II

Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a yau Laraba 25 ga watan Satumbar 2024 yayin taron inganta fasaha a jihar Kano, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya taya Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II murnar sake dawowa sarautar jihar mai daraja.

"Dawo da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan sarauta na daya daga cikin abin da ya faranta min rai a rayuwa ta "
"Ina mai sake taya ka murna a karo na biyu."

- Nasir El-Rufai

Gwamnonin da suka halarci taron a Kano

Taron da aka shirya domin bunkasa yankin Arewacin Najeriya ya samu halartar manyan yan siyasa da gwamnoni.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano da na Katsina, Dikko Umaru Radda.

Sai kuma gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare da sauran manyan mutane daga yankin Arewacin kasar.

Kara karanta wannan

Matawalle ya fadi yadda ya kwaci Dauda Lawal daga hannun EFCC, ya kalubalance shi

Diyar marigayi Ado Bayero ta sake magana

Kun ji cewa 'yar marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ta koka kan yadda mutane suka dira kansu saboda neman taimako da suka yi.

Zainab Ado Bayero ta ce dan Adam yana neman taimako ne musamman idan wadanda suke da hakkin kulawa da shi suka guje shi.

Diyar marigayin ta bayyana yadda aka rika kwatanta da malalaciya saboda ta nemi taimako inda ta ce kwata-kwata ba haka ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.