Yajin Aiki: Kungiyar ASUU Ta Ba Gwamnatin Tarayya Sabon Wa'adi, Ta Kafa Sharadi

Yajin Aiki: Kungiyar ASUU Ta Ba Gwamnatin Tarayya Sabon Wa'adi, Ta Kafa Sharadi

  • Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta yi barazanar shiga yajin aiki saboda gazawar gwamnatin tarayya na cika mata ɓuƙatun ta
  • ASUU ta ba gwamnatin wa'adin kwanaki 14 da ta warware matsalolin da ke tsakaninsu ko ta tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar nan
  • Shugaban ƙungiyar da ya ba da wa'adin ya koka kan yadda gwamnati ba ta yin wani kataɓus domin aiwatar da yarjeniyoyin da ke tsakaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU), ta ba gwamnatin tarayya sabon wa'adin kan shiga yajin aiki.

ASUU ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 don warware dukkanin matsalolin da ke tsakaninsu waɗanda aka daɗe ana tattake waje a kansu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana matsalar da sojoji ke fuskanta

ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki
ASUU ta ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 Hoto: Prof. Tahir Mamman, ASUU
Asali: UGC

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ASUU ta ce kan yajin aiki?

Emmanuel Osodeke ya bayyana takaicinsa kan rashin yin wani kataɓus daga wajen gwamnati.

Shugaban ya koka kan yadda take jan ƙafa wanda a cewarsa hakan na kawo matsaloli a cikin jami’o’in gwamnati, rahoton Tribune ya tabbatar.

"Bisa ga abubuwan da ke faruwa, ASUU ta amince ta ba gwamnatin Najeriya ƙarin wasu kwanaki 14, bayan kwanaki 21 da ta ba da a baya tun daga ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, 2024."
"A cikin waɗannan kwanakin dole a warware dukkanin wasu batutuwan da aka daɗe ana tattake waje a kansu bisa gamsuwar mambobin ƙungiyar."
"Ka da a ɗorawa ƙungiyar alhaki kan yajin aikin da zai iya biyo baya saboda gazawar gwamnati na yin amfani da sabuwar damar da ASUU ta ba da domin warware rikicin."

Kara karanta wannan

CBN ya hango sauƙin da ƴan Najeriya za su samu, ya yi magana kan matatar Ɗangote

- Farfesa Emmanuel Osodoke

ASUU ta shiga yajin aiki a GSU

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) reshen jami'ar jihar Gombe ta sanar da fara yajin aiki.

ASUU ta shiga yajin aikin ne a yammacin ranar Laraba, 11 ga watan Satumban 2024, bayan gwamnatin jihar Gombe ta gaza biya mata buƙatun ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng