Gwamnatin Bauchi Ta Gabatar da Sabon Kasafin Kudi a Majalisa, Ta Fadi Aikin da Za Ta Yi

Gwamnatin Bauchi Ta Gabatar da Sabon Kasafin Kudi a Majalisa, Ta Fadi Aikin da Za Ta Yi

  • Gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta gabatar da ƙarin kasafin kuɗi a gaban majalisar dokoki
  • Gwamnatin ta gabatar da kasafin kuɗin na N94.6bn ne domin neman majalisar dokokin ta amince da shi
  • Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar ne ya karanta buƙatar gwamnan a zaman majalisar na ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Gwamnatin Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta miƙa sabuwar buƙata a gaban majalisar dokokin jihar.

Gwamnatin ta Bala Mohammed ta gabatar da ƙarin kasafin kuɗi na Naira biliyan 94.676 ga majalisar dokokin jihar domin neman amincewa da shi.

Gwamnatin Bauchi ta gabatar da kasafin kudi
Gwamna Bala Mohammed na son majalisa ta amince da karin kasafin kudi Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce buƙatar da mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar, Babayo Akuyam ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya aika saƙo ga majalisar dattawa kan sabuwar shugabar alƙalan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gabatar da takardar ne a madadin Gwamna Bala Mohammed.

Meyasa Gwamna Bala ya miƙa buƙatar?

Babayo Akuyam ya bayyana cewa gwamnan yana neman amincewar ne kamar yadda sashe na 122 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 ya tanada, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Ya ce Gwamna Bala yana son gaggauta aiwatar da ayyuka masu muhimmanci da nufin inganta jin daɗin mutanen jihar Bauchi.

"Gwamnan ya himmatu wajen inganta ababen more rayuwa da inganta fannin kiwon lafiya da ilimi."

- Babayo Akuyam

Majalisar Bauchi za ta kafa kwamiti

Bugu da ƙari, majalisar ta fara shirin kafa kwamitin samar da abinci da abinci mai gina jiki da nufin magance matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a jihar.

Da yake gabatar da ƙudirin, Babayo Akuyam, ya bayyana cewa kwamitin zai mayar da hankali ne wajen samar da abinci mai gina jiki ga ƴan jihar Bauchi masu rauni musamman mata, yara, da ƴan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahun Adamawa, ya faɗi watan da zai fara biyan sabon albashin N70,000

Gwamnan Bauchi ya magantu kan rikicin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Bala Muhammed ya ce babu wanda zai kunna wuta a jihar Bauchi kuma ya ci galaba saboda akwai isasshen ruwan kashe wutar.

Ya faɗi haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin gudanarwa (NWC) na jam’iyyar PDP ta ƙasa a fadar gwamnatinsa da ke birnin Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng