Cire Tallafin Fetur: Tsohon Hadimin Jonathan Ya Fadi Matsalar Shawarar Dangote

Cire Tallafin Fetur: Tsohon Hadimin Jonathan Ya Fadi Matsalar Shawarar Dangote

  • Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa Goodluck Jonathan, Doyin Okupe ya ce shawarar cire tallafin fetur bai taso ba
  • Ya fadi haka ne a matsayin martani da ya yi ga shawarar da fitaccen dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya ba gwamnatin tarayya
  • Alhaji Dangote na ganin sauran tallafin da ake biya na jawo asara mai dimbin yawa, saboda haka ya ga dacewar cire shi duka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Doyin Okupe, tsohon hadimin shugaba Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana rashin amincewa da shawarar da fitaccen dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya ba gwamnati.

Kara karanta wannan

Baki har kunne: Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya samu manyan nasarori a cikin mako 1

Alhaji Dangote ya shawarci gwamnatin kasar nan da cewa lokaci ya yi da za ta janye sauran tallafin man fetur da ta ke bayarwa.

Kamfanin
Doyin Okupe ya ce shawarar Dangote kan janye sauran tallafin fetur zai jawo takura Hoto: Dangote Industries|NNPCL Limited
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Dangote wanda ya bayyana ra'ayinsa a birnin New York da ke Amurka na ganin kasar nan na asarar Tiriliyoyi wajen biyan tallafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okupe ya ga rashin dacewar shawarar Dangote

Jaridar The Cable ta ruwaito tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Doyin Okupe ya ce man fetur shi ne ruhin kasar nan.

Saboda haka ya ke ganin bai dace a rika kira ga gwamnatin tarayya ta janye dukkanin tallafin da ta ke bayarwa a bangaren ba.

Okupe na maraba da matatu irin na Dangote

Doyin Okupe ya bayyana cewa man fetur na shafar rayuwar jama'ar kasar nan kai tsaye; daga mai kudi har talaka.

Kara karanta wannan

"Ka cire tallafi gaba daya": Dangote ya shawarci Tinubu ana tsaka da korafi

Tsohon daraktan yakin neman zaben Peter Obi na da yakinin samar da matatu a cikin kasar nan zai taimaka wajen wadata yan Najeriya da fetur.

Dangote ya bayar da shawarar cire tallafin fetur

A baya mun ruwaito cewa shahararren dan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote ya shawarci gwamnatin kasar nan ta gaggauta cire sauran tallafin man fetur da ta ke biya.

A ganin fitaccen dan kasuwar, dole sai gwamnati ta daina biyan tallafin fetur baki daya al'amuran kasar nan za su daidaita, duk da kukan da ake da matsalar da cire tallafi ya jefa jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.