Izala Ta Yi Babban Rashi: Alhaji Abdullahi, Mahaifin Ministan Noma Ya Rasu

Izala Ta Yi Babban Rashi: Alhaji Abdullahi, Mahaifin Ministan Noma Ya Rasu

  • Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya karbi rayuwar Alhaji Abdullahi Sabi, mahaifi ga karamin ministan noma da samar da abinci
  • Ma'aikatar noma ta tarayya, wadda ta fitar da sanarwar ta ce mahaifin Sanata Aliyu Abdullahi ya rasu ya na da shekaru 100 a duniya
  • Wannan rasuwar dai ta girgiza kungiyar JIBWIS kasancewar marigayin na daga wadanda suka assassa Izala a masarautar Borgu, jihar Neja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Ma'aikatar noma da samar da abinci ta fitar da sanarwar rasuwar Alhaji Abdullahi Sabi, mahaifi ga ministan ma'aikatar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi.

Alhaji Abdullahi Sabi, mahaifin mai girma karamin ministan ma'aikatar noma da samar da abinci ta tarayya ya rasu yana da shekaru 100 a duniya.

Kara karanta wannan

Fitacciyar mawakiyar Musulunci a Najeriya, Rukayat Gawat ta rigamu gidan gaskiya

Sanata Aliyu: Allah ya yiwa mahaifin karamin ministan noma da samar da abinci Rasuwa.
Mahaifin ministan noma da samar da Abinci, Sanata Aliyu ya kwanta dama. Hoto: @sabialiyu
Asali: UGC

Mahaifin ministan noma ya rasu

Mahaifin ministan ya rasu ne a unguwar New Bussa, da yammacin ranar Litinin, 23 ga Satumba, 2024 kamar yadda ministan ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce an gudanar da Sallar Jana'izarsa da misalin karfe 2:00 na ranar ranar Talata, 24 ga Satumba, 2024, a fadar Gbemusu, Sabuwar Bussa, Jihar Neja.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Abdullahi, wanda aka haifa a shekarar 1924 ya kasance hakimin Luma a karkashin masarautar Borgu, New Bussa, jihar Neja.

Kungiyar Izala ta yi babban rashi

A sakon da kungiyar Jamaatul Izalatul Bidia Wa Ikamatul Sunnah (JIBWIS) ta fitar a shafinta na Facebook, ta nuna matukar alhininta na rasuwar Alhaji Abdullahi.

Sanarwar ma'aikatar noma ta nuna cewa Alhaji Abdullahi na daga cikin wadanda suka assassa kungiyar Izala (JIBWIS) a masarautar Borgu kuma ya rike mukamin shugabanta.

Kara karanta wannan

Dorinar Ruwa ta yi ajalin dogarin Sarki, Gwamna ya kadu

Sanarwar da Sanata Sabi Abdullahi ya fitar a madadin iyalan mamacin ta tuna cewa Alhaji Abdullahi ya taba rike kansilan sa ido na karamar hukumar Borgu.

Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin “mutum mai hakuri da juriya,” kuma tsohon Sarkin Borgu, Musa Mohammed Kigera III ne ya nada shi Hakimin Malale, garin kakarsa.

Mahaifiyar Yar'adua ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar Hajiya Dada, mahaifiya ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'Adua.

An bayyana cewa Hajiya Dada ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya yau Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024, tana da shekaru 102 a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.