Ma'aikata Za Su Wataya: Tinubu Ya Sanya Ranar Fara Biyan Sabon Albashin N70000

Ma'aikata Za Su Wataya: Tinubu Ya Sanya Ranar Fara Biyan Sabon Albashin N70000

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sanar da cewa za ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma'aikata daga 29 ga Yuli, 2024
  • Wata sanarwa daga ofishin shugabar ma'aikatan tarayya ta ce gwamnatin ta kuma amince da sake tsarin albashin wasu ma'aikata
  • An rahoto cewa sanya lokacin aiwatar da sabon albashi ya zo bayan gwamnati da kungiyar kwadago sun rattaba hannu a yarjejeniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu za ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi daga ranar 29 ga Yuli, 2024.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da sake fasalin tsarin albashi ga malamai, likitoci, sojoji da sauran ma'aikatan gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahun Adamawa, ya faɗi watan da zai fara biyan sabon albashin N70,000

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta aiwatar da sabon mafi karancin albashi
Gwamnatin Tinubu ta sanya lokacin fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi.
Asali: Facebook

Za a aiwatar da sabon albashi

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnati da kungiyar kwadago suka rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna kan sabon mafi karancin albashin N70,00 inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwa daga ofishin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, mai dauke da sa hannun shugaban yada labarai da hulda da jama’a, Eno Olotu ta yi karin bayani kan lamarin.

Sanarwar ta ce kwamitin da ke kula da albashin ma’aikatan ya amince cewa za a fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi daga ranar 29 ga watan Yulin 2024.

Gwamnati ta duba tsadar rayuwa

The Punch ta rahoto cewa wannan yarjejeniyar na daga cikin kudurorin da aka cimmawa a karshen taron kwamitin a Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata.

A cewar sanarwar, kwamitin ya kuma bayar da shawarar a biya albashin ma’aikatan da gwamnatin tarayya ta dakatar har zuwa ranar 28 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga taron FEC ana rade raɗin za a kori wasu ministoci, bayanai sun fito

Kwamitin bisa jagorancin shugabar ma'aikatan tarayya, Didi Walson-Jack, ya bayyana cewa gwamnati ta yi la'akari da yanayin tattalin arzikin kasar kafin ta yanke shawarar.

Albashi: Gwamnati ta gargadi ma'aikatu

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban sakatare a ma'aikatar kwadago, Ismaila Abubakar a madadin gwamnatin tarayya ya gargadi kamfanoni masu zaman kansu

Gwamnatin tarayya ta yi gargadi ma'aikatu masu zaman kansu kan cewa ba za ta amince da biyan ma'aikaci kasa da N70,000 ba bayan dokar sabon mafi karancin albashin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.