Tsadar Rayuwa: Gwamna Ya Rage Ranakun Aiki, Za a Rabawa Ma'aikata Tallafi

Tsadar Rayuwa: Gwamna Ya Rage Ranakun Aiki, Za a Rabawa Ma'aikata Tallafi

  • Gwamnatin jihar Osun ta bi sahun ta jihar Ekiti wajen rage kwanakin aikin ma'aikatan jihar saboda tsadar rayuwa
  • Gwamna Ademola Adeleke ne ya ce an dauki matakin ne domin saukaka halin kunci da hauhawar farashi ya jefa jama'a
  • Gwamnatin ta ware wasu kwanaki ga kowane mataki na ma'aikata, sannan za a rika ba su tallafi na tsawon watanni biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya amince da rage ranakun aiki ga ma'aikatan gwamnatin jihar saboda tsadar rayuwa.

Gwamna Adeleke ya kuma amince da ci gaba da raba tallafin rage radadin rayuwa har na watanni biyu ga ma'aikatan saboda halin da ake ciki na matsi.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya yabi Tinubu bayan daukar kwakkwaran matakin inganta ilimi

Ademola
Gwamnan Osun ya rage kwanakin aiki Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin Osun ta dauki matakin ne domin ya zo daidai da tsarin gudanarwarta na inganta rayuwar ma'aikata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanakin aikin da aka rage a Osun

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnati ta amince ma'aikatan da ke aiki daga mataki na daya zuwa 10 su rika zuwa aiki sau uku a mako.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamna Adeleke ya fitar, Olawale Rasheed, ta ce su kuma ma'aikatan da ke aiki daga mataki na 12 zuwa 17 su rika zuwa aiki sau hudu.

Za a raba tallafi ga ma'aikatan Osun

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya yi albishir ga ma’aikata na ci gaba da raba masu kayan tallafi har na tsawon watanni biyu.

Ya ce za a ci gaba da raba tallafin ne kafin a fara biyan ma’aikatan mafi karancin albashin N70,000 da gwamnati ta sahale.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na shirin kare hakkin yan Najeriya, za ta yaki masu tauye mudu

Gwamna ya ragewa ma'aikata kwanakin aiki

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Ekiti ta bayyana rage kwanakin aiki ga ma'aikatanta da ke kowane mataki saboda halin da tsadar man fetur ta jefa jama'ar kasar nan a ciki.

Lamarin ya biyo bayan karin kudin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi, lamarin da ya jawo karuwar farashi tare da kawo hauhawar farashin ababen hawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.