"Sauki Zai Samu": Ƴan Kasuwa Sun Gano Hanyar Karya Farashin Man Fetur a Najeriya
- Ƴan kasuwa sun tabbatar wa ƴan Najeriya cewa da zaran sun fara ɗauko mai kai tsaye daga matatar Ɗangote farashi zai sauka
- Mai magana da yawun kungiyar dillalan mai IPMAN, Chinedu Ukadike ya ce sun fara tattaunawa da matatar domin fara kasuwanci
- Wannan kalamai na zuwa ne yayin farashin litar fetur ta ƙara tashi bayan NNPCl ya fara jigilar mai daga matatar attajirin ɗan kasuwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Manyan dillalan mai a Najeriya sun tabbatar da cewa farashin fetur zai sauka matuƙar aka ba su damar yin kasuwanci kai tsaye da matatar Ɗangote.
Wannan kalamai na diillalan na zuwa ne bayan kamfanin mai na kasa NNPCL ya fara jigilar ɗauko mai daga matatar Ɗangote sannan ya sayarwa ƴan kasuwa.
Tashar Channels tv ta ce farashin litar fetur ya kai ₦950 a Legas da kewaye, yayin da da ya cike N1000 a Arewacin Najeriya duk da ana tace shi a cikin gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dillalai sun fara shirin tsallake NNPCL
Sai dai kakakin kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya ce sun fara tataunawa domin duba yiwuwar sayo mai kai tsaye daga matatar Ɗangote.
Da yake bayani a cikin shirin safe na gidan talabijin yau Talata, Ukadike ya ce ƙungiyar IPMAN ita ke da kaso 85 na gidajen man da ake da su a ƙasar nan.
Ya ce da zarar sun gama tattaunawa kuma ƴan kasuwa suka fara ɗauko fetur kai tsaye daga matatar Ɗangote, farashi zai sauka a Najeriya.
"Man etur zai yi arha" - IPMAN
"Idan aka bar IPMAN ta zama mai dogaro da kanta wajen sayo mai, farashi zai sauka, saboda mu ƴan kasuwar mai za mu fara gasa a tsakanin mu."
"Lokacin da Ɗangote ya fara samar da man dizil, IPMAN ya nema kuma nan da nan muka fara shiga muna ɗauko kaya, ba daɗewa farashi ya sauka daga N1,600 yanzu ya dawo N1000 zuwa N1,100."
- Chinedu Ukadike.
Tinubu ya yi kuskure a cire tallafin fetur
A wani rahoton kuma tsohon shugaban NESG ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya biyo hanya mai gargada wajen cire tallafin man fetur a Najeriya.
Kyari Bukar ya ce kamata ya yi shugaban ƙasa ya rika cire 5% na tallafin mai duk bayan watanni shida don kaucewa halin da ƴan Najeriya za su shiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng