Dakaru Sun Kara Yin Gagarumar Nasara, Sojoji Sun Hallaka Abokin Bello Turji

Dakaru Sun Kara Yin Gagarumar Nasara, Sojoji Sun Hallaka Abokin Bello Turji

  • Sojojin kasar nan sun kara hallaka jagoran yan ta'adda da su ka addabi yankin Zamfara da kewaye da hare-haren ta'addanci
  • An kashe dan ta'adda Kachalla Sani Black da ya'yansa guda biyu tare da kama makamai masu tarin yawa da wasu makudan kudi
  • Wannan nasarar na zuwa bayan dakarun sojan kasar nan sun yi nasarar sheke daya daga cikin iyayen gidan Turji, Halilu Sububu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Jami'an tsaron kasar nan sun samu gagarumar nasara a yakin da su ke na kawar da manyan yan ta'adda daga doron kasa.

A wannan jikon, dakarun sun hallaka Kachalla Sani Black, wanda abokin fitinannen dan ta'adda, Bello Turji ne a Zamfara.

Kara karanta wannan

Baki har kunne: Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya samu manyan nasarori a cikin mako 1

Nigerian Army
An sake kashe abokin Bello Turji Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Mai sharhi kan al'amuran tsaron kasar nan, Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa kafin mutuwarsa, Kachalla Black ya addabi jama'a wajen kai hare-hare a Zamfara da kewaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe abokin Bello Turji

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa jami'an sa kai dake Magama Mai Rake a karamar hukumar Maru, bisa tallafin sojojin kasar nan ne su ka tarfa Kachalla Sani Black.

Rahotanni sun bayyana cewa kasungurmin dan ta'addan na da yan ta'adda sama da 150 da ke aiki a karkashinsa, inda su ke kai hare-haren ta'addanci kan mazauna yankin.

Da wa aka kashe abokin Bello Turji?

Harin da jami'an tsaron kasar nan su ka kai Zamfara ya yi nasarar kashe Kachalla Sani Black da yaransa maza guda biyu.

Daga cikin abubuwan da aka samu daga wannan hari akwai miyagun makamai kamar AK-47 da PKT da kuma tarin kudin da ba a bayyana nawa ne ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun aika 'yan ta'adda 8 lahira, an ceto wanda aka yi garkuwa da su

Sojoji sun kashe abokan ta'addancin Turji

A baya mun ruwaito cewa jami'an rundunar tsaron kasar nan ta bayyana kokarin dakarunta wajen kawo karshen kasungurmin dan ta'adda, Halili Sububu, tare da daukar alkawarin magance rashin tsaro.

Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da ya bayyana haka ya shawarci masu taimakon yan ta'adda su guji yin haka, inda ya ce nan gaba kadan za a kashe dan ta'adda Bello Turji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.