"Muna Kwana a kan Titi": Halin da Mutanen Maiduguri Suka Shiga bayan Ambaliya

"Muna Kwana a kan Titi": Halin da Mutanen Maiduguri Suka Shiga bayan Ambaliya

  • Biyo bayan ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri da Jere a jihar Borno, mazauna garin da dama sun koma kafa tanti na kan tituna
  • Ambaliyar ruwa bayan batsewar madatsar ruwan Alau a ranar 10 ga watan Satumba, ta haddasa barna da raba iyalai da muhallansu
  • Wasu daga cikin wadanda ambaliyar ta raba su da gidajensu, sun koma kwana a kan titi bayan rufe sansanonin gwamnati da ke jihar Borno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Ambaliyar ruwa da ta mamaye birnin Maiduguri na jihar Borno ta raba dubunnan daruruwan mutane da muhallansu, lamarin da ya tilasta su kwana a kan titi.

Wadanda ambaliyar ta shafa musamman a Maiduguri da Jere sun koma kafa tanti a kan tituna bayan da jami'an gwamnati suka rufe wasu sansanoni.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Gwamnatocin jihohi 9 da suka ba Borno tallafin Naira biliyan 1.1

'Yan Maiduguri da ambaliya ta shafa sun ba da labarin halin da suke ciki yanzu
Mutanen Maiduguri da ambaliya ta raba su da muhallansu na cikin gagari.
Asali: UGC

A cewar kwamishinan watsa labarai da tsaron cikin gida na Borno, Usman Tar, ambaliyar ta shafi gidaje 30,000 wanda ya shafi mutane 600,000 a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da mutanen Maiduguri ke ciki

Da farko dai an ce gwamnatin jihar ta kafa sansanoni da dama domin ba da matsugunni ga wadanda ruwan ya daidaita. Amma bayan ruwan ya ja, an rufe wasu sansanonin.

Jami'an gwamnatin jihar sun bukaci wadanda ke zaune a wadannan sansanoni da su tattara komatsansu su koma gidajensu tun da yanzu ruwan ya ragu

To sai dai kuma da yawa daga cikin wadanda suka tsira sun ce gidajensu ba sa zaunuwa a yanzu, lamarin da ya sa suka kafa matsuguni na wucin gadi a kan tituna.

Wadanda suka rasa muhallansu sun kafa tanti na wucin gadi a yankuna kamar Muna, Gambarou, Custom, da kuma tsohuwar Maiduguri, inda suke ci gaba da neman mafaka.

Kara karanta wannan

Yadda mutane sama da 100 su ka rasu a manyan iftila'I 4 a Arewacin Najeriya

"Mun rasa muhalli" - Malam Yusuf

Wani dattijo mai shekaru 60 da ambaliyar ruwa ta shafa, Malam Yusuf Aliyu, ya bayyana abin da ya faru a lokacin da ya kafa tanti a kan titin a rukunin gidaje 505.

Malam Yusuf Aliyu ya ce:

“Tun ina karami na ke zaune a unguwar nan, ban taba ganin bala’i irin wannan ba. "Muna buƙatar wurin da za mu rika kwana don haka muka kafa tantin gidan sauro a kan titi."

Wani wanda ya abin ya shafa, Babagana Jibrin daga tsohuwar Maiduguri, ya ce ya dade a sansanin gwamnati da ke kwalejin gwamnati a Maiduguri kafin a rufe shi gabanin bude makarantar.

“An ba mu kudi da abinci mu koma gida mu jira kwamitin agaji domin tantance gidana da ya ruguje. Ba ni da inda zan je yanzu. Shi ya sa na kafa tanti” a cewar Babagana.

Sabuwar matsala na tunkarar Borno

Kara karanta wannan

Ambaliya: Majalisar dinkin duniya ta ba da tallafin dalolin kudi ga mutanen Maiduguri

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta ce akwai yiwuwar a samu barkewar cututtuka a Maiduguri, sakamakon ambaliyar da ta afku.

NMA ta yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron lafiyar mutane a Maiduguri, jihar Borno.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.