Yan Bindiga Sun Bindige Limamin Masallaci Har Lahira a Abuja, Sun Sace Mutum 1
- An shiga alhini bayan wasu yan bindiga sun hallaka limanin masallaci a birnin Tarayya Abuja
- Maharan sun kai harin ne a daren jiya Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024 bayan fitowa sallar Isha
- Bayan kisan limamin, yan bindiga sun yi awon gaba da wani mai harkar Sufuri, Alhaji Abubakar Danfulani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wasu yan bindiga sun kai wani mummunan hari a birnin Tarayya da ke Abuja.
Yayin harin, maharan sun kuma sace wani limamin masallaci a yankin Mpape da ke birnin.
Yan bindiga sun hallaka limani a Abuja
Aminiya ta tabbatar da cewa maharan sun kuma sace wani mai harkar sufuri, Alhaji Salisu Danfulani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024 da ya tsoratar da yan yankin.
Wani mai suna Nasir Ahmed ya ce maharan sun kai harin ne dai dai lokacin da aka fito sallar Isha, cewar rahoton Sahara Reporters.
Nasiru ya ce limamin ya yi kokarin tserewa amma aka yi rashin sa'a wani daga cikin yan bindiga ya harbe shi har lahira.
An kai gawar limamin mai suna Mallam Ahmed Maidara gida da ke unguwar Gwagwa inda aka yi jana'izarsa.
Yan sanda sun shirya dakile ta'addanci
Wannan na zuwa ne bayan Sufeton yan sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun ya yi garanbawul ga manyan jami'an tsaro a wasu jihohi domin dakile ta'addanci.
IGP Kayode Egbetokun ya ba da umarnin canza kwamishinonin yan sanda a jihohin Rivers, Delta da kuma birnin tarayya Abuja.
Tankar mai ta yi bindiga a Abuja
Kun ji cewa wata tanka maƙare da man fetur ta fashe a kan dogon titin Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 23 ga watan Satumba.
Rahotanni sun nuna cewa wuta ta kama sosai bayan fashewar tankar, lamarin da ya sa mutane guduwa domin neman tsira da rayuwarsu.
Wani ma'aikaci a ɗaya daga cikin asibitocin Maitama ya bayyana cewa an kawo waɗanda lamarin ya rutsa da su domin ba su kulawa da yi masu magani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng