"Na Rantse da Kur'ani kan Zargin Ta'addancin Zamfara:" Matawalle Ya Yi Martani

"Na Rantse da Kur'ani kan Zargin Ta'addancin Zamfara:" Matawalle Ya Yi Martani

  • Tsohon Zamfara, Bello Matawalle ya sake barranta kansa da matsalar tsaron da ke wakana a jihar bayan zargin da ake yi masa
  • Matawalle ya bayyana haka ne bayan gwamnatin Dauda Lawal Dare ta zarge shi da hana zaman lafiya a jihar Zamfara
  • Karamin Ministan tsaron kasar nan ya ce a yanzu, gwamna Dauda Lawal ba zai iya abin da ya yi a lokacin ya na gwamna ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi kakkausan martani kan masu zarginsa da hannu cikin ta'addancin da ke addabar mazauna Zamfara.

Kara karanta wannan

Matawalle ya fadi yadda ya kwaci Dauda Lawal daga hannun EFCC, ya kalubalance shi

Matawalle, wanda shi ne karamin Ministan tsaro ya bayyana cewa shi ne gwamna daya tilo da ya iya yin rantsuwar rashin alaka da ta'addanci.

dauda
Dr. Matawalle ya rantse kan alaka da ta'adanci Hoto: Dauda Lawal/Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

A hira da ya yi da kafar talabijin Channels, Dr. Bello Matawalle ya kara da cewa babu wani a gwamnatinsa lokacin ya na gwamna da bai sha rantsuwa kan rashin alaka da ta'addanci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta'addanci: Dalilin rantsewar Bello Matawalle

Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya ce ya rantse da Al-kur'ani mai tsarki domin tabbatar da cewa ba shi da alaka ko jin dadin ta'addancin da ke gudana a jiharsa.

Ya bayyana cewa ya sha rantsuwar saboda ya san zuciyarsa fes ta ke, kuma ba shi da sha'awar abin da ke faruwa a kasarsa.

Matawalle ya kalubalanci gwamnan Zamfara

Tsohon gwamnan Zamfara, Dr. Bello Matawalle ya kalubalanci gwamna mai ci, Dauda Lawal Dare kan ya yi rantsuwa makamanciyar wacce ya yi a lokacinsa.

Kara karanta wannan

Baki har kunne: Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya samu manyan nasarori a cikin mako 1

Dr. Matawalle na ganin rashin rantsuwar wata manuniya ce kan cewa gwamnatin Zamfara na da hannu cikin ta'addancin da jihar ke fuskanta.

APC ta zargi gwamnatin Zamfara da ta'addanci

A wani labarin kun ji cewa jam'iyyar APC, reshen jihar Zamfara ta roki gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta baci a Zamfara biyo bayan zargin da su ka yi na hannun gwamnati cikin ta'addanci.

Jami'in hulda da jama'a na APC a jihar, Yusuf Idris da ya yi zargin, ya ce gwamnatin Dauda Lawal Dare da kawo tasgaro a yakin da gwamnatin tarayya ke yi da rashin tsaro a Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.