Tinubu Ya Rarrashi Yan Najeriya, Ya yi Alkawarin Samun Saukin Rayuwa
- Gwamnatin tarayya ta kara yin kira na musamman ga yan Najeriya kan halin wahalar rayuwa da ake ciki a kasar nan
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawari nan gaba kadan yan Najeriya za su murmure a kan halin da suke ciki
- Bola Tinubu ya yi magana kan matsalolin da suka dabaibaye kasar nan wanda suka haɗa da rashin tsaro da yawaitar talauci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi kira na musamman ga yan kasa kan halin wahala da ake ciki a Najeriya.
Gwamnatin ta bukaci yan Najeriya su kara hakuri domin an kusa kai wa ga samun sauƙin rayuwa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Didi Esther Walson-Jack ce ta wakilci shugaban kasar yayin wani taro a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya ce an kusa samun sauki
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce yasan cewa cire tallafin man fetur da rage darajar Naira sun jefa mutane a wahala.
The Nation ta wallafa cewa shugaban kasar ya bukaci a kara hakuri saboda nan gaba kadan za a fara cin moriyar tsare tsaren shi.
Shugaban kasar ya yi alkawarin ne yayin da al'ummar Najeriya ke fama da tsadar rayuwa kuma suna shirin zanga zanga a Oktoba.
Tinubu ya fadi wasu matsalolin Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce a halin yanzu bayan matsalar tattali akwai rashin tsaro, talauci garkuwa da mutane.
Saboda haka ya ce akwai bukatar daukar mataki ta fuskoki da dama domin fitar da Najeriya cikin matsala.
Bola Tinubu ya kara da cewa dole sai an samo mafita ga asalin abin da ya haifar da matsalolin tsaro a kasar nan idan ana son samun zaman lafiya mai dorewa.
Talaka ya amince da Tinubu inji Barau
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana bayan jami'yyar APC ta lashe zaben gwamna a jihar Edo.
Sanata Barau Jibrin ya ce nasarar jami'yyar APC a zaɓen alama ce da ke nuna cewa talaka na goyon bayan tsare tsaren Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng