Magana Ta Girma: 'Yan Majalisa Sun Bukaci Tsige Shugaban EFCC kan Yahaya Bello

Magana Ta Girma: 'Yan Majalisa Sun Bukaci Tsige Shugaban EFCC kan Yahaya Bello

  • Yan majalisar jihar Kogi sun bukaci a gaggauta tsige shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede kan rikicin hukumar da Yahaya Bello
  • Hakan na zuwa ne bayan hukumar EFCC ta yi yunkurin kama tsohon gwamna Yahaya Bello a gidan gwamnatin jihar Kogi da ke Abuja
  • Majalisar jihar Kogi ta ce sam EFCC ba ta nuna kwarewa ba wajen tunkarar Yahaya Bello kuma ta zargi hukumar da yunkurin kisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Lamura na kara dagulewa tsakanin EFCC da Yahaya Bello kan badaƙalar kudi da ake zargin tsohon gwamnan.

A makon da ya wuce hukumar EFCC ta yi yunkurin cafke Yahaya Bello inda aka yi harbe harbe amma ba su kama shi ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya rarrashi yan Najeriya, ya yi alkawarin samun saukin rayuwa

Yahaya Bello
An bukaci tsige shugaban EFCC kan Yahaya Bello. Hoto: Economic and Financial Crime Commission|Yahaya Bello
Asali: Facebook

Biyo bayan haka, Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa majlisar jihar Kogi ta bukaci a tsige shugaban EFCC, Ola Olukoyede.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Kogi ta bukaci tsige shugaban EFCC

Punch ta wallafa cewa dan majalisar jihar Kogi, Akus Lawal ne ya mika kudirin tsige shugaban EFCC, Ola Olukoyede a gaban majalisar jihar.

Biyo bayan haka, kudirin ya samu karɓuwa wajen dan majalisa Jacob Olawunmi kafin majalisar ta amince da shi.

Majalisar Kogi ta ce EFCC ba ta nuna kwarewa ba

Majalisar jihar Kogi ta ce hukumar EFCC ba ta nuna kwarewa wajen yunkurin kama Yahaya Bello ba sam.

Yan majalisar sun ce harba harsashi da EFCC ta yi a wajen ya nuna cewa hukumar ta wuce wajen da dokar kasa ta ajiye ta.

Majalisa ta zargi EFCC da yunkurin kisa

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta fadi yadda aka yi gumurzu wajen yunkurin kama Yahaya Bello

Majalisar jihar Kogi ta ce abin da ya faru a gidan gwamnatin Kogi a ranakun 17 da 18 akwai barazanar kisa a ciki.

Yan majalisar Kogi sun ce cikin lamarin akwai barazana ga rayuwar gwamna Usman Ahmed Ododo da kuma yunkurin kashe Yahaya Bello.

Yahaya Bello ya ce ya hadu da EFCC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ya baro ofishin EFCC salin-alin ba tare da jami'ai sun titsiye shi da tambayoyi ba.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Ohiare Michael ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar bayan Yahaya Bello ya ce ya mika wuya ga EFCC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng