Dorinar Ruwa Ta Yi Ajalin Dogarin Sarki, Gwamna Ya Kadu

Dorinar Ruwa Ta Yi Ajalin Dogarin Sarki, Gwamna Ya Kadu

  • Wani dattijo mai shekaru 60 ya gamu da ajalinsa a jihar Kebbi bayan dorinar ruwa ta kai masa farmaki a ranar Lahadi
  • Marigayin mai suna Mallam Usman Maigadi ya kasance dogarin sarkin Yauri, Muhammad Zayyanu-Abdullahi
  • Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin da kuma masarautar Yauri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - An shiga firgici bayan dorinar ruwa ta yi ajalin dogarin Sarkin Yauri da ke jihar Kebbi.

Marigayin mai suna Usman Maigadi ya rasa ransa ne a lambun sarkin, Dr. Muhammad Zayyanu-Abdullahi.

Dorinar ruwa ta yi ajalin dogarin sarki a Kebbi
An shiga jimami bayan dorinar ruwa ta yi ajalin dogarin sarkin Yauri a jihar Kebbi. Hoto: Masarautar Kebbi, Getty Images.
Asali: Facebook

Dorinar ruwa ta hallaka dogarin sarkin Yauri

Vanguard ta ruwaito cewa dabbar ta yi tsammanin marigayin na kokarin zuwa inda ta ke domin cutar da jaririyarta ne

Kara karanta wannan

Fitacciyar mawakiyar Musulunci a Najeriya, Rukayat Gawat ta rigamu gidan gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotannin sun tabbatar da cewa marigayin mai shekaru 60 ya gamu da tsautsayin ne a ranar Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024.

Lamarin ya faru ne a kauyen Tillo da ke karamar hukumar Yauri yayin da dattijon ke kamun kifi, cewar rahoton Daily Post.

Shugaban karamar hukumar Yauri, Alhaji Abubakar Shu'aibu ya ce an binne marigayin kamar yadda adinin Musulunci ya tanadar.

"Tuni aka gudanar da salla da kuma binne marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar."

- Abubakar Shu'aibu

Gwamna Idris ya kadu da mutuwar dattijon dogarin

Gwamna Nasir Idris na jihar Kebi ya nuna alhini kan rasuwar marigayin a karamar hukumar Yauri.

Sanarwar na kunshe ne a cikin wasikar da hadiminsa, Alhaji Ahmed Idris ya fitar game da tsautsayin.

Sanarwar ta ce Gwamna Nasir Idris ya kadu ta lamarin inda ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da kuma masarautar Yauri.

Kara karanta wannan

Ta Dikko dakin kara: Katsina ta cika shekaru 37 da kafuwa, an fara shirin biki

Gwamna Idris zai biya albashin N70,000

Kun ji cewa Gwamna Nasir Idris ya yi alƙwari da zaran an kammala tsara komai, zai fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi a Kebbi.

Gwamna Idris ya ce gwamnatinsa ta shirya fara biyan sabon albashin ba kamar yadda wasu ke yaɗawa ba.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da kungiyar kwadago NLC ta kai masa ziyara har gidan gwamnatinsa da ke Birnin Kebbi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.