“Ka Cire Tallafi Gaba Daya”: Dangote Ya Shawarci Tinubu Ana Tsaka da Korafi
- Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya yi magana kan cire tallafin man fetur inda ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara
- Dangote ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta cire maganar biyan tallafin man fetur gaba daya domin daidaita lamura
- Hakan ya biyo bayan korafe-korafe da ake ta yi bayan cire tallafin man fetur da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shahararren dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya shawarci Bola Tinubu kan cire tallafin man fetur.
Dangote ya ce wannan shi ne lokacin da ya dace Tinubu ya cire tallafin gaba daya domin daidaita lamura.
Dangote ya yi magana kan cire tallafi
Attajirin ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabjin na Bloomberg a jiya Litinin 23 ga watan Satumbar 2024 da Punch ta bibiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote ya ce maganar cire tallafin mai abu ne mai sarkakkiya inda ya ce da za ran gwamnati ta cire tallafi, mutane za su kara farashi.
Ya ce hakan zai tilasta gwamnati biyan kudin da bai kamata tana cigaba da biya ba.
"Ina tunanin wannan shi ne lokacin da ya dace a rabu da maganar tallafi saboda duka kasashe sun tsayar da ba da tallafi."
- Aliko Dangote
"Gwamnati ba za ta iya biya ba" - Dangote
Dangote ya ce cigaba da biyan tallafin mai ba zai dore ba inda ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da biya ba, kamar yadda TheCable ta ruwaito.
Ya kara da cewa wannan ya ragewa gwamnati ta duba ko ta cigaba da biyan tallafin ko kuma ta dakatar da shi.
Dillalan mai sun guji matatar Dangote
Kun ji cewa matatar man Dangote ta koka kan yadda dillalan mai da suka yanke shawarar cigaba da shigo da mai daga ketare.
Matatar da zargi dillalan da shigo da fetur da ba shi da kyau da kuma inganci da zai kawo nakasu a harkar mai.
Wannan na zuwa ne bayan manyan dillalan mai guda uku a Najeriya sun dauki matakin dauko man daga kasashen waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng