Gwamna Ya Bi Sahun Adamawa, Ya Faɗi Watan da Zai Fara Biyan Sabon Albashin N70,000

Gwamna Ya Bi Sahun Adamawa, Ya Faɗi Watan da Zai Fara Biyan Sabon Albashin N70,000

  • Gwamna Alex Otti zai fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 daga watan Oktoba, 2024 a jihar Abia
  • Kwamishinan yaɗa labarai, Okey Kanu ne ya sanar da hakan jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa ta jiha ranar Litinin
  • Kanu ya bayyana wasu ayyuka da gwamnatin ta shirya yi kamar duba marasa lafiya, kula da mata masu ciki da gwaje-gwaje duk a kyauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Gwamnatin jihar Abia ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alex Otti ta bayyana cewa za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi daga watan Oktoba.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Okey Kanu ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, 23 ga watan Satuma yayin da yake zantawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

Ana raɗe raɗin gwamna na shirin sauya sheƙa, ciyamomi sun fice daga jam'iyyar PDP

Alex Otti.
Gwamnatin Abia ta shirya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a watan Oktoba Hoto: Alex Otti
Asali: Facebook

Kanu ya ce gwamnatin ta cimma wannan matsaya ne a taron majalisar zartaswa ta jiha (SEC) wanda Gwamna Otti ya jagoranta, Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Okay Kanu ya ce dukkan ma'aikata a kowane mataki za su fara ganin sabon albashi mafi ƙanƙanta da aka amince da shi watau akalla N70,000.

Gwamna Otti zai gina sababbin kotuna 17

Kwamishinan ya kara da cewa a ƙoƙarin gwamnatin Abia na karfafa harkokin shari’a, za ta fara gina kotuna 17 a fadin kananan hukumomi 17 na jihar.

Ya kuma bayyana cewa a makon gobe ma’aikatar lafiya za ta shirya gudanar da aikin duba marasa lafiya kyauta a garin Ugwunagbo, rahoton Vanguard.

Kanu ya ce mutane za su samu damar ganawa da ƙwararrun likitoci domin neman shawarin lafiya, kula da mata masu juna biyu da yara da gwaje-gwaje duk a kyauta.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su wataya: Tinubu ya sanya ranar fara biyan sabon albashin N70000

Gwamnan Abia zai gana da ƴan wasa

Har ila yau kwamishinan yaɗa labaran Abia ya ce Gwamna Otti ya shirya ganawa da ƴan wasan motsa jiki da suka sanya jihar alfahari a gasar wasanni musamman Onyinyechi Mark.

Gwamnan zai gana da Miss Onyinyechi Mark wacce ta lashe zinari a fanin kilo 61 da Miss Esther Nworgu wacce ita ma ta samu azurfa a ajin kilo 41 domin karfafa guiwar sauran yan wasa.

Gwamnatin Tinubu ta faɗi lokacin fara biyan N70,000

A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta fadi lokacin da fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 zai soma aikin bayan an amince da ƙarin.

Kwamitin tsarawa da gyara albashin ma'aikata (NSIWC) ya yi zama na musamman kan fara biyan mafi ƙarancin albashin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262