Dangote: Ƴan Kasuwa Za Su Yi Maganin NNPCL a Karya Farashin Man Fetur
- Kungiyar dillalan fetur ta kasa ta ce matakin da NNPCL ya dauka na zama mai dakon fetur daga matatar Dangote ya ba su mamaki
- Kakakin kungiyar IPMAN na kasa, Cif Chinedu Ukadike ya bayyana cewa su na sa ran fara sayo fetur kai tsaye daga matatar
- A zantawarsa da Legit, sakataren kudi na kungiyar, Musa Yahya Maikifi ya ce za a samu saukin fetur idan sun fara dauko shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana yakinin cewa za ta iya fara sayen fetur kai tsaye daga matatar Dangote.
Wani zagaye ya nuna yadda wasu gidajen sayar da mai a Abuja ke rufe na tsawon akalla watanni uku saboda karancin fetur a kasar nan.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kakakin kungiyar IPMAN na kasa, Cif Chinedu Ukadike ya ce yanzu haka ana tattaunawa kan ba yan kasuwa damar dauko fetur kai tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
IPMAN na shirin ganawa da matatar Dangote
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa ta ce a wannan makon ne ta ke shirin gana wa da wasu wakilan matatar man Dangote kan ba su damar dauko fetur kai tsaye.
Kakakin kungiyar IPMAN na kasa, Cif Chinedu Ukadike ya bayyana farin ciki kan yadda matatar Dangote ta fara neman masu sha'awar dakon fetur.
Matatar Dangote: IPMAN ta fadi laifin NNPCL
Sakataren kudi na kungiyar ta IPMAN, Musa Yahya Maikifi ya shaida wa Legit cewa kamfanin NNPCL ya ba su mamaki da ya zama shi ne mai dakon fetur daga matatar Dangote.
Mai Kifi ya ce sun so a bar su, sayi man fetur din kai tsaye daga matatar Dangote, domin ta haka ne yan kasar nan za su samu sauki.
Karancin fetur: IPMAN ta dora laifin kan NNPCL
A baya kun ji cewa kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta zargi NNPCL da jawo wahalar man fetur da karancinsa da ya addabi jama'ar kasar nan, biyo bayan gazawar kamfanin.
Shugaban IPMAN da ke wurin sauke fetur na Ore, Shina Amoo ya ce NNPCL ya fi shekara uku bai ba su fetur din da ake bukata ba duk da cewa su na da gidajen mai sama da 3,000 a Najeriya.
Asali: Legit.ng