Fetur: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Shawarci Tinubu Ya Sauka daga Kujera

Fetur: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Shawarci Tinubu Ya Sauka daga Kujera

  • Matsalolin man fetur da su ka dabaibaye kasar nan ya sa an fara ganin rashin amfanin shugaba Tinubu a matsayin Ministan Fetur
  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NRM, Felix Osakwe ne ya bayyana haka, inda ya ce yan Najeriya na cikin wahala
  • Mista Osakwe ya bayyana cewa shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari da shugaban kasa sun gaza fitar da kasa daga matsalar fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Felix Osakwe ya shawarci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ajiye mukamin Ministan man fetur.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban NESG ya faɗi kuskuren Tinubu da ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala

Felix Osakwe, wanda ya nemi mukamin Tinubu a zaben 2023 ya bayyana cewa alamu sun bayyana na gazawar shugaban kasa wajen rike mukamin.

Tinubu
An shawarci Tinubu ya ajiye mukamin Ministan fetur Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Mista Osakwe ya zargi shugaba Tinubu da kamfanin mai na kasa (NNPCL) da jefa jama'ar kasar nan cikin wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu ya gaza:" Felix Osakwe

Jaridar The Cable ta tattaro tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NRM, Felix Osakwe ya ce Bola Tinubu ya gajiya wajen shawo kan matsalolin da su ka addabi bangaren fetur.

Ya bayyana cewa shugaban kasar da shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari sun gaza yin abin da ya dace wajen rage wahalhalun man fetur da ake fuskanta a Najeriya.

Ministan fetur: Osakwe ya caccaki Tinubu

Jigo a jami'yyar NRM, Felix Osakwe ya ce bai ga dalilin da zai sa shugaban kasa, Bola Tinubu ya kasa zabar wani a matsayin ministan man fetur ba.

Kara karanta wannan

"Ba maganar kwasar kudi ba ne": Tinubu ya fadi dalilin zuwansa 'Aso Rock'

Mista Osakwe ya yi mamakin yadda a cikin yan kasar nan sama da miliyan 200, Tinubu ya kasa amince wa da dauko wanda ya cancanci rike mukamin.

"Tinubu ya jefa mutane cikin wahala:" Kyari

A wani labarin kun ji cewa tsohon shugaban NESG, Bukar Kyari ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tafka babban kuskure da ya jefa jama'a cikin kuncin rayuwa.

Bukar Kyari ya ce kamata ya yi shugaban kasa ya sahale a rika cire 5% na tallafin man fetur duk wata, amma cire tallafin lokaci guda ce ta kawo matsalar da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.