Matasa Sun Lakaɗawa Soja Dukan Tsiya, Sojoji Sun Fusata
- Rahotanni na nuni da cewa wasu matasa a jihar Oyo sun lakaɗawa wani sojan Najeriya duka bisa zargin kisan kai
- Matasan sun zargi sojan ne da harbe wani jami'in NSCDC mai suna Olapade Segun a wani waje a yankin Bodija a jihar Oyo
- An ruwaito cewa wasu daga cikin jami'an sojin Najeriya ne suka iske wajen da gaggawa domin ceto rayuwar sojan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Ana zargin wasu matasa da lakaɗawa sojan Najeriya dukan tsiya a yankin Bodija na jihar Oyo.
An ruwaito cewa sojojin Najeriya sun dura wajen da matasan suke yiwa sojan duka yayin da lamarin ke faruwa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa akwai alamar rundunar sojin Najeriya na bincike kan lamarin domin gano gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi soja da kisan kai a Oyo
Wasu matasa a wani gidan wasa a jihar Oyo sun zargi wani sojan Najeriya da harbe wani jami'in NSCDC mai suna Olapade Segun.
Matasan sun ce sojan ya zaro bindiga ya harbe jami'in NSCDC ne yayin da suka samu sabani mai tsanani a gidan wasan.
Matasa sun lakaɗawa soja dukan tsiya
An ruwaito cewa bayan sojan ya harbe Olapade Segun, ya yi niyyar guduwa amma sai matasan suka tare shi.
Daga nan kuma matasan suka hau sojan da dukan kawo-wuka inda suka tara masa jini da majina.
Sojoji sun fusata kan dukan jami'insu
Bayan fara dukan sojan ne sai wasu jami'an soja suka taho wajen a fusace suka tarwatsa taron matasan suka ceto rayuwar sojan.
Haka zalika rahotanni na nuni da cewa sojoji na zuwa ofishin NSCDC wanda hakan ke nuni da cewa suna bincike ne a kan lamarin.
Sojoji sun kama yan ta'adda a Taraba
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Taraba.
Sojojin na rundunar 'Operation Whirl Stroke' sun cafke waɗanda ake zargin ne bayan sun samu bayanan sirri kan ayyukansu na barna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng