Fusatattu matasa sun yiwa soja mugun duka kan kashe wani mai siyar da takalma a Kaduna

Fusatattu matasa sun yiwa soja mugun duka kan kashe wani mai siyar da takalma a Kaduna

- Hankula sun tashi yayinda wani soja ya soki wani mai siyar da takalma da wuka

- Lamarin dai ya afku ne a babbar kasuwar Sheikh Gumi a ranar Alhamis

- Hakan ya tunzura matasa a wajen inda suka ji ma sojan mummunan rauni

An shiga rudani a babbar kasuwar Sheikh Gumi a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu lokacin da wani soja ya soki wani mai siyar da takalma da wuka.

Hakan ya sa fusatattun matasa a kasuwar suka far masa inda suka ji masa mummunan rauni.

Shaidu da abun ya faru a idanunsu sun bayyana cewa sojan wanda ke sanye da kayan gida ya dauki matakin ne bayan wani sabani ya shiga tsakaninsa da mai siyar da takalmin.

Ba a san cikakken abunda ya haddasa musun nasu ba amma lamarin ya faru da misalin karfe 2:30 na rana a .

“Wani soja ne ya chaki mai siyar da takalma da wuka bayan wani musu sannan matasan da ke wajen auka far masa inda suka ji ma sojan mummunan rauni a kai kafin a cece shi,” in ji wani shaida wanda ya bayyana kansa a matsayin Salisu.

KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa da mutane sun saki basaraken da suka sace a Kano

Da aka tuntubi kakakin yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo, ya yi alkawarin samo cikakken bayani tare da tuntubar majiyarmu ta Daily Trust.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel