Seaman Abbas: DHQ Ta Yi Magana kan Zargin Tsare Sojan Ruwa na Shekara 6
- Hedkwatar tsaro ta ƙasa ta yi martani kan zargin cewa an tsare wani sojan ruwa har na tsawon shekara shida bisa rashin adalci
- Daraktan yaɗa labarai na DHQ ya bayyana cewa ba a taɓa kama Seaman Abbas ba kamar yadda matarsa ta yi zargi
- Ya yi bayanin cewa za a gayawa ƴan Najeriya komai kan lamarin da zarar an kammala binciken da ake gudanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce Seaman Abbas Haruna, wanda ake zargin an tsare shi tsawon shekara shida, ba a taɓa kama shi ba.
Matar Abbas Haruna, Hussaina Iliya, ta je wani gidan rediyo mai farin jini a Abuja inda ta zargi sojoji da tsare mijinta bisa rashin adalci tun shekarar 2018.
Hakan ya sanya babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, suka bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me DHQ ta ce kan tsare Seaman Abbas?
A wata hira da wakilin jaridar The Punch a ranar Asabar, daraktan yaɗa labarai na DHQ, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya ce ba a taɓa kama Abbas Haruna ba.
"Ba a taɓa kama shi ba. Mutane kawai suna yin surutu ne kan abin da ba haka yake ba."
- Birgediya Janar Tukur Gusau
Da aka tambaye shi inda yake tun lokacin da matarsa ta yi iƙirarin cewa ya shafe shekara shida a hannun sojoji, Tukur Gusau ya ce za a bayyana hakan bayan an kammala bincike.
"A halin yanzu ana ci gaba da bincike. A lokacin da rahoton binciken ya kammala, za mu sanar da ƴan Najeriya abin da ya faru da kuma inda yake."
- Birgediya Janar Tukur Gusau
DHQ ta musanta zargin matar Abbas
Da aka ƙara matsa masa lamba kan maganar matar, Tukur Gusau ya ce matar Abbas Haruna ta san ba a kama mijinta ba.
"Ta san ba a kama mijinta ba. A lokacin da ya dace, za mu sanar da mutane abin da ya faru."
- Birgediya Janar Tukur Gusau
NEF ta yi Allah wadai kan tsare Seaman Abbas
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Northern Elders Forum (NEF) ta bayyana damuwa kan halin da jami'in rundunar sojin ruwa na kasa, Seaman Abbas Haruna ke ciki.
A martanin da ta yi, ƙungiyar NEF ta ce akwai damuwa da alamomin tambaya kan yadda ake bautar da jami'an da ke kokarin kare martabar ƙasar nan.
Asali: Legit.ng