Manyan Dillalan Mai Sun Fitar da Matsaya da Matatar Dangote Ta Sake Farashi

Manyan Dillalan Mai Sun Fitar da Matsaya da Matatar Dangote Ta Sake Farashi

  • Matatar man Dangote ta koka kan yadda dillalan mai da suka yanke shawarar cigaba da shigo da mai daga ketare
  • Matatar da zargi dillalan da shigo da man wanda ba shi da kyau da kuma inganci da zai kawo nakasu a harkar mai
  • Wannan na zuwa ne bayan manyan dillalan mai guda uku sun dauki matakin dauko man daga kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Matatar man Dangote ta nuna damuwa kan halin da ake ciki yanzu game da shigo da mai kasar.

Matatar Dangote da sauran matatu sun koka kan yadda manyan dillalan mai suka yanke shawarar shigo da man daga ketare.

Kara karanta wannan

Girgizar kasa a Abuja: Gwamnatin tarayya ta bayyana matakan da ta dauka

Matatar Dangote ta koka da matakin dillalan mai a Najeriya
Matatar Dangote ta caccaki dillalan mai kan shigo da kaya daga ketare. Hoto: Tom Saater.
Asali: Getty Images

Matatar Dangote ta soki dillalan mai

Punch ta ruwaito cewa matataun sun bayyana cewa hakan zai kara daga darajar dala da sake kassara Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatun sun ce man da za a kawo daga ketare kwata-kwata bai kai wanda matatar Dangote za ta samar a Najeriya kyau ba.

Wannan na zuwa ne bayan manyan dillalan mai uku sun dauki matakin shigo da man fetur daga kasashen waje.

Adadin litocin da dillalan za su kawo

Akalla dillalan na tsammanin shigo da litocin mai miliyan 141 zuwa Najeriya daga ketare.

Yayin da take martani, matatar Dangote da kungiyar masu tace danyen mai sun caccaki matakin da dillalan suka dauka.

"Wadannan dillalan mai suna kawo man da ba shi da kyau ko kadan kuma maras inganci, idan aka bar su hakan ba zai tsaya ba."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na shirin kare hakkin yan Najeriya, za ta yaki masu tauye mudu

"Mu na da man isasshe kuma mai kyau amma sun ki amincewa da shi, suna son cigaba da shigo da man kuma hakan ba zai yiwu ba."

Cewar wata majiya

Rikici ya yi tsami tsakanin Dangote da NNPCL

Kun ji cewa an sake samun alkaluma mabanbanta kan man fetur da kamfanin mai na NNPCL ya dauka daga matatar Dangote.

Matatar Dangote ta ce ta ba kamfanin NNPCL man fetur har lita miliyan 111 tun da ta fara ba kamfanin mai a ranar Lahadi da ta gabata.

Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa matatar Dangote za ta iya fitar da tataccen mai ne da bai wuce lita miliyan 16.8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.