“Ba Maganar Kwasar Kudi ba ne”: Tinubu Ya Fadi Dalilin Zuwansa ‘Aso Rock’

“Ba Maganar Kwasar Kudi ba ne”: Tinubu Ya Fadi Dalilin Zuwansa ‘Aso Rock’

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan dalilin zuwansa fadar shugaban kasar Najeriya domin cire shakku
  • Tinubu ya ce aiki ne ya kawo shi fadar shugaban kasa ba wai neman kudi da amfani da damar ta wani hanya ba
  • Shugaban Najeriya ya kuma roki alumma hadin kai domin tabbatar da kawo sauyi a kasar Najeriya baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fadi musabbabin zuwansa fadar shugaban kasar Najeriya.

Bola Tinubu ya ce ya zo fadar 'Aso Rock' ne domin bautawa kasa ba wai cika aljihunsa da kudin kasar ba.

Tinubu ya fadi dalilin zuwansa fadar shugaban kasa
Bola Tinubu ya ce aiki ne ya kawo shi fadar shugaban kasa ba kudi ba. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya fadi shirin gwamnatinsa a Najeriya

Kara karanta wannan

"Na san komai": Tinubu ya magantu game da halin kunci, ya fadi silar shan wahala

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da shafin fadar shugaban kasa ta fitar a shafin X a yau Juma'a 2 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin tabbatar da inganta rayuwar al'umma da samar da ayyuka nagari.

Ya ce ya ba da kulawa na musamman wurin samar da abinci da wutar lantarki da kuma inganta tattalin arzikin kasar.

Shugaban ya yaba da irin goyon baya da ya ke samu daga mambobin kungiyar tsofaffin shugabannin Majalisar Tarayya.

Tinubu ya fadi dalilin zuwansa 'Aso Rock'

"Ban zo nan domin neman kudi ba, na zo ne domin yin aiki, na bukaci kuri'u kuma yan Najeriya sun ba ni."

- Bola Tinubu

Tsofaffin 'yan majalisa sun hadu da Tinubu

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ken Nnamani a madadin tawagar ya yabawa gwamnatin Bola Tinubu a kokarinta na kawo karshen matsalolin kasar.

Kara karanta wannan

'Ya so biya mana kudin jirgi,' Yan kwadago sun tono sirrin zamansu da Tinubu

Nnamani ya taya Tinubu nasarar zama shugaban kasa inda ya ce wannan shi ne karon farko da suka fara ganawa.

Tinubu ya yi magana kan halin kunci

A wani labarin, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ya sani ana cikin wani hali a Najeriya inda ya zargi gwamnatocin baya.

Shugaba Tinubu ya ce dukan wannan hali da aka shiga na da nasaba da irin matakan da aka dauka a baya a Najeriya.

Shugaban ya bukaci hadin kai daga masu ruwa da tsaki da sauran al'umma domin ciyar da Najeriya gaba kamar sauran kasashe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.